Home / Kasuwanci / A Kamo Dikko Inde Da Mutane Biyu- Kotun Tarayya

A Kamo Dikko Inde Da Mutane Biyu- Kotun Tarayya

Wata babbar kotun Gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin kama tsohon shugaban hukumar kwastan na Nijeriya Abdullahi Dikko Inde saboda kin halartar kotun da ya yi.

Kotun dai ta gayyaci tsohon shugaban hukumar kwastan ta Nijeriya domin amsa tambayoyi sakamakon kararsa  tare da wadansu mutane biyu da hukumar yaki da aikata cin hanci da rashawa da al’ amuran da suka danganci hakan (ICPC).

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu, lokacin da take bayar da umarnin a kamo Dikko Inde a ranar yau Litinin ta bayyana cewa Lauyan Dikko Inde, babban lauyan Nijeriya Solomon Akuma wanda a ranar da aka zauna kotun aka dage zaman sai yau 17 ha watan 02, 2020. Lauyan ya yi alkawarin cewa zai tabbatar wanda yake karewa ya halarci kotun a yau, amma sai kawai ya zo ma kotun da wata takardar rahoton rashin lafiya cewa Dikko na cikin tsananin rashin lafiya kuma an kwaltar da shi a kasar Ingila, a birnin Landan.

Mai shari’a Ojukwu ta bayyana cewa kamar yadda aka bayar da rahoton cewa rashin lafiyar Dikko an bada adireshi kamar haka lamba N6 Ahmed Musa Crescent Jabi, Abuja bai yi daidai da irin ikirarin da lauyan yake yi ba na cewa an kwantar da Dikko Dikko a wani asibitin birnin Landan.

Mai shari’ar ta kuma fahimci cewa idan har an tabbatar da cewa gaskiya ne Dikko na can a kwance  a wani Asibitin birnin Landan to za a iya dakatar da umarnin kama shi.

Mai shari’ar ta kara da cewa ta bada umarnin a kamo Dikko Inde a kuma gabatar da shi a gaban kotu a ranar 16 ha watan Maris, 2020 wanda shi ne ranar da aka Sanya domin ci gaba da wannan shari’ar.

A cikin kara mai lamba “FHC/ABJ/CR/21/2019, an Sanya sunan Dikko tare da wadansu mutane biyu na farko tsohon mataimakin shugaban hukumar kwastan mai kula da harkokin kudi da mulki Garba Makarfi da Umar Hussaini, wani lauya da ke da kamfanin harkokin lauya na Capital Law firm, a matsayin wadanda ake kara.

Dikko, Makarfi da Hussaini na cikin wadanda ake zargi da umartar manajan darakta na kamfanin Cambial Limited, Yemi Obadeyi, da ya biya kudi naira biliyan 1.1 (N1.100,952,380.96). A cikin asusun ajiyar kudi na kamafanin capital Law office “na kammala harkar tsaro” da aka sayi wani wurin da ya zama gidan zaman manyan jami’an hukumar kwastan ta Nijeriya.

Hussaini dai an ce ya rarraba wadannan kudin a cikin asusun ajiyar kudi daban daban wanda sakamakon hakan a saka masa da kudi Dala miliyan uku (3).

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.