Home / Lafiya / Akwai Yuwuwar Sake Kakaba Dokar Kulle A Jihar Kaduna – El- Rufa’i

Akwai Yuwuwar Sake Kakaba Dokar Kulle A Jihar Kaduna – El- Rufa’i

Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, ya bayyana cewa akwai yuwuwar sake kakaba wa Jihar Kaduna dokar kulle ta hana fita saboda kin bin ka’idojin hana yaduwar Cutar Korona.
Gwamna Malam Nasiru, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta bbc hausa, inda ya ce alkalumman masu dauke da cutar na karuwa ne sakamakon kin bin ka’idar da aka Sanya ta gujewa yin cinkoson jama’a da yin amfani da Takunkumin rufe baki da hanci.
“Takunkumin rufe baki da hanci zai taimaka wajen hana daukar cutar da kuma yadawa wasu mutane da mutum yaje tare da su, amma jama’a basa bin wadannan ka’idojin da aka Sanya saboda son zuciya kawai”.
“Sai kaga mutum ba Takunkumin rufe baki da fuska amma idan an yi masa magana sai kaga mutum ya fito da Takunkumin a cikin aljihunsu wai yana da shi amma ba zai Sanya shi ba”.
A game da batun bude kasuwanni da Masallatan da ake yin Sallah sau biyar a kowace rana kuwa, sai Gwamnan ya amsa tambaya da cewa “To mun ji amma gara mutum ya yi bara da ake cewa yan kasuwa sun fara yin bara, gara mutum ya yi bara yana da rai da a same shi ya mutu”.
Ya ci gaba da cewa Bama son yawan masu cutar ya fi karfin asibitocin da muke da su a Jihar nan, ko kuma na cibiyoyin kula da masu dauke da cutar Korona.
“Idan ka bude kasuwa wuri ne na mutane da yawa idan mutum daya mai dauke da cutar ya shiga kasuwa shi kadai zai iya ba mutane dubbai, kuma haka lamarin yake idan an bude masallatai na yin Sallar jam’i guda biyar a kullum da zarar wanda yake dauke da cutar ya shiga nan ma zai harbi jama’a da dama.” Inji Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i.
Ga dukkan mai sha’awar saurararon hirar za a ci gaba da yada ta a kafar yada labarai ta bbc hausa a ranar Asabar kamar yadda suka bayyana.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.