Home / Labarai / An Ba Tsohon Kakakin Rundunar Sojan Nijeriya, Kukasheka Sarkin Yakin Ketare A Katsina

An Ba Tsohon Kakakin Rundunar Sojan Nijeriya, Kukasheka Sarkin Yakin Ketare A Katsina

An Ba Tsohon Kakakin Rundunar Sojan Nijeriya, Kukasheka Sarkin Yakin Ketare A Katsina
Mustapha Imrana Abdullahi
Kanwan Katsina kuma Hakimin Ketare, Alhaji Usman Bello Kankara, ya bayar da sarautar Sarkin Yakin Ketare ga tsohon kakakin rundunar sojan Nijeriya, Birgediya Janar Sani Usaman Kukasheka mai ritaya.
 Bayanan da muke samu sun bayyana cewa Kukasheka na cikin muhimman  mutanen da suka samu Sarautu daban daban bayan da mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya amince da a ba su sarautun.
Wannan bayar da sarautun  wani bangare ne domin bikin murnar cika shekaru Ashirin (20) da nadin da mai martaba Sarkin Katsina ya yi wa Alhaji Usman Bello Kankara, wanda ya kasance babban jami’in hukumar kwastan ne ta kasa kafin bashi sarautar.
Sauran da aka ba sarautar sun hada da Awwal Usaman Bello Kankara Ciroman Kanwa, Alhaji Ibrahim Sama’ila Sarkin Fada, Bishir Sama’ila aatsayin Sallama, Alhaji Mannir Abubakar Garkuwa, Lawal Abnas Zanna sai Munauwar Ibrahim matsayin Tafida, Abdulrahman Bello Wazirin ayyuka,Usman Yusuf matsayin Muhti da kuma Musa Isma’il Mani a matsayin Sarkin Waka.
Sauran su ne Alhaji Rabi’u Wada Ketare da aka ba Hasken Fada, Mohammed Usman Bello Sarkin Hawa, Isa Mohammed da ke aiki a hukumar kula da ilimin bai daya ta Jihar Katsina a matsayin Talba, Labaran Bello Kankara a matsayin Wambai,Alhaji Sule Ketare Waziri sai Malam Imrana Kankara Khadimul Islam, Sanusi Labo Ajiyan Kanwa da kuma Hashimu Jobe a matsayin Sardauna.
Kanwan Katsina, ya kuma bukaci wadanda aka ba wannan sarautu da su ci gaba da taimakawa masarautar Ketare, Karamar hukumar Kankara, Jihar Katsina da Nijeriya baki daya.
Kamar yadda ya ce an ba su wannan sarauta ne sakamakon irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban masarautar da kuma yankin na Ketare baki daya.
Sarkin Fada, Alhaji Ibrahim Samaila, ne zai yi jawabin godiya a madadin wadanda aka ba sarautun a matsayin mambobin wannan masarauta, duk sun tabbatar da cewa za su yi amfani da dimbin kwarewarsu domin samar da ingantaccen ci gaba da wannan masarauta ta Hakimin Ketare.
Majiyarmu ta bayyana mana cewa nan gaba kadan za a bayyana ranar da za a yi bikin nadin wadannan sarautu.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.