Home / Local GOVERNMENTS / An Gano Ma’aikata, Yan Fanshon Bogi Dubu 22,000 A Jihar Bauchi

An Gano Ma’aikata, Yan Fanshon Bogi Dubu 22,000 A Jihar Bauchi

 Imrana Abdullahi
Kwamitin binciken da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa domin binciken harkar fanshon Jihar sun bayyana wa manema labarai a garin Bauchi cewa sun samu nasarar gano yan fanshon bogi mutane dubu 22,000 da suka ce Gwamnatin na samun rarar naira miliyan 225.
An dai kafa kwamitin domin binciken lambar sirrin asusun ajiyar banki (BVN) na ma’aikatan Jihar da na masu karbar fansho inda aka gano mutane ma’aikatan bogi dubu 22,448 na ma’aikatan bogi da yan fansho a matakin Jiha da kananan hukumomi da ake kusa makudan kudin da suka kai miliyan 225,519000,737 tsakanin watan Okutoba, 2019 zuwa Yuni, 2020.
Shi dai wannan kwamitin Gwamna Jihar ne Bala Abdulkadir Mohammed  ya kafa shi karkashin jagorancin Sanata Adamu Ibrahim Gumba inda kwamitin ya bayyana hakan bayan kammala binciken a wajen wani taron manema labarai a Bauchi.
Mista Abdon Dalla Gin wanda mai taimakawa Gwamnan Bauchi ne a kan harkokin ma’aikata, ya wakilci shugaban kwamitin.
Mista Dalla Gin ya ce kwamitin ya yi aiki da ma’aikatan Gwamnati dubu 41, 448 da suka hadar da masu aiki da yan fansho da suke kan takardun biyan Albashi na Gwamnati da kuma kananan hukumomi 20 da suke a Jihar
Mista Dalla Gin ya ce ” cikin ma’aikata dubu 41,448 da kuma yan fansho da aka ba Kwamitin guda dubu 22,448 ba su so gaban kwamitin ba domin a tantance su ta hanyar tabbatar da su a bayyane su ne da kuma lambar sirri na asusun ajiyar Banki ta (BVN), kamar yadda kwamitin ya bukata.
Musta Dalla Gin ya ce har sai da suka yi shela ta hanyar sanarwa kan cewa su zo domin tantance su a rediyo da sauran kafafe aka yi sanarwar amma ba a kansu ba sam.
Mista Dalla ya ci gaba da cewa sun samu jimillar Judi naira miliyan 225, 519,737 a matsayin rarar kudi ga Gwamnati daga watan Okutoba 2019 zuwa Yuni 2020.
Daga ciki an samu mutane 112 na jiha da 284 na ma aikatan kananan hukumomi da suka kasa zuwa domin a tantance su, ko dai saboda mutuwa
“Mun gano mutane 312 da suka mutu a matakin kananan hukumomi masu karbar fansho da jimlar kudin da suke karba ya kai miliyan 9 wanda a halin yanzu tuni aka cire su a jerin biyan fansho a Jihar.
Mr.Dalla Gin ya kuma tabbatarwa manema labarai cewa sun gano wadansu ma’aikata 11 da suke karbar Albashi sau biyu ta hanyar duba bayanan kudinsu na banki na watan Yuli da Satumba, an kuma samu ma’aikatan da suke karbar albashin Jiha Jiha suna karbar kudin shirin N – Power
Ma aikatar lafiya za ta Sanya kwararru domin gudanar da bincike a kan ga wani ma’aikacin da aka gano yana da tabin hankali”, inji Dalla Gin.
Mr. Dalla Gin ya yaba da irin hangen nesan Gwamna Bala Mohammed ta yadda ya bayar da cikakkiyar dama ga kwamitin ya gudanar da aikinsa.
Mr Dalla Gin ya kara da cewa kwamitin dai ya samu nasarar kammala aikinsa duk da ainihin dakatarwar da aka yi masa sau biyu saboda matsalar cutar Korona, aka kuma shirya sakatariyar kwamitin.
Kwamitin dai na da mutane 20 da suka wakilci muhimman kungiyoyin kwadago daban daban.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.