Home / Labarai / An kaddamar da kungiyar ‘yan sintiri a  Danja. 

An kaddamar da kungiyar ‘yan sintiri a  Danja. 

Daga Abdullahi Sheme

  A makon da ya gabata ne a ka kaddamar da kungiyar’yan sintiri na garin Danja da ke karamar hukumar Danja
An dai yi wannan taron ne a dakin taro na karamar hukumar da ke cikin garin Danja Jihar Katsina.
A jawabinsa Sakataren kungiyar Alhaji Lawal Dako Danja ya karanto tarihin kungiyar da irin nasarorin da  kungiyar ta samu da yadda aka zabo mutanen da zasu gudanar da aikin sintirin.
 Ya ce mutane ne amintattu kuma masu gaskiya da rikon amana wadanda suka sa karfinsu domin sadaukar da rayuwarsu don kare al’umma da dukiyoyinsu.
 sai ya gargade su da su  guji yawan sanya wasa ko wani ha’inci ko ramuwar gayya a wajen gudanar da aikinsu kuma su tsare gaskiya kowa ya yi laifi su kama shi su mikawa hukuma.
Alhaji Dako ya ciga ba da nuna godiyarsu ga Shugaban riko na karamar hukumar Danja Alhaji Hamza Umar Sabuwar kasa, yadda yake aiki tukuru wajen kafuwar wannan kungiya Mai albarka, “babu shakka Alhaji Hamza ya zama dole a yaba masa a kan wannan kungiya ya Kuma mika godiyarsu ga dukkan masu ruwa da tsaki na karamar hukumar tare da ya ba ma Sarkin kudun katsina hakimin Danja Alhaji M T Bature da dukkan jami’an tsaron yankin musamman Baturen ‘yan sanda na karamar hukumar watau DPO S M Gawuna wajen kokarin shi da Kuma irin shawarar da yake ba kungiyar.
Daga karshe ya godema dukkan Al’ummar karamar hukumar sannan ya yi kira garesu da suba kungiyar ‘yan sintirin hadin Kai da sauran jami’an tsaro yankin wajen lalubo batagari kuma su guji yanke hukunci wato daukar doka a hannunsu.
Jama’a da dama sun gabatar da jawabi a wajen taron inda suka yi ta fadakarwa a kan al’amuran tsaro domin ciyar da al’umma gaba.

About andiya

Check Also

APC RELOCATES TO NEW STATE HEADQUARTERS IN GUSAU, ZAMFARA

The Zamfara State chapter of the All Progressives Congress APC has today relocated to its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.