Home / Labarai / An Sace Yan Makarantar Firamare Da Malamansu A Birnin Gwari

An Sace Yan Makarantar Firamare Da Malamansu A Birnin Gwari

An Sace Yan Makarantar Firamare Da Malamansu A Birnin Gwari
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta sake samun rahoton sace Yan Makaranta tare da Malamansu a karamar hukumar Birnin Gwari da ke Jihar kaduna.
Kamar dai yadda Gwamnatin ta fitar da wani bayanin cewa ta samu rahoton sace wadansu yara yan makarantar Firamare da makamansu a Rema cikin karamar hukumar Birnin Gwari.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun Kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida Malam Samuel Aruwan.
Kamar yadda takardar ta bayyana cewa bayanin farko ya nuna faruwar lamarin ne a wata makarantar Firamare da ke karamar hukumar.
Gwamnatin ta ci gaba da bayanin cewa su na nan a kan yin aikin samar da cikakkun bayanai a game da yawan dalibai da malaman da aka kwasa don haka za a fitar da cikakkun bayanai nan gaba kadan da an kammala bincike.

About andiya

Check Also

Between El-Rufai and parents of abducted students is empathy

  Contrary to the mischief in some sections of the media, the bond between Governor …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *