Home / Labarai / ASD Ya Samu Nasara A Kotu, Shugaban Yan Sanda Zai Biya Miliyan 2

ASD Ya Samu Nasara A Kotu, Shugaban Yan Sanda Zai Biya Miliyan 2

ASD Ya Samu Nasara A Kotu, Shugaban Yan Sanda Zai Biya Miliyan 2

Daga Wakilinmu
Babbar kotu a Jihar Kaduna ta yanke hukuncin cewa tsarewar da aka yi wa Alhaji Sani Dauda (ASD), Alkali Malam Almisri da shehu sani Dauda ya sabawa doka.
Tun farko dai an samu takaddamar aure ne tsakanin Nasiba Shehu Sani Dauda da kuma Abubakar Musa Abubakar, wanda dalilin hakan aka tsare uban Yarinyar Alhaji Sani Dauda (ASD) da kuma Malamin da ya Daura auren Alkali Malam Almisri da shehu sani Dauda a ofishin yansanda a cikin garin kaduna wanda kan hakan ne suka shigar da kara domin take masu yanci.
Sun dai yi karar shugaban yan sandan Nijeriya da Abubakar Musa Abubakar ne a gaban babbar kotun jihar Jihar suna neman hakkin su sakamakon tsarewar da aka yi masu.
Kamar yadda Lauyan da ke tsayawa Alhaji Sani Dauda da sauran wadanda aka tsare Barista Maxwell Kyon ya shaidawa manema labarai a harabar kotun Jim kadan bayan yanke hukuncin cewa ” hakika kotun ta tabbatar da cewa tsarewar da aka yi wa Alhaji Sani Dauda, Malam Almisri da shehu Sani Dauda ya sabawa Dokar kasa domin babu wani hurumin da za a yi hakan kamar yadda doka ta tanadar”.
“Kotun ta ce abin da kwamishinan yan sanda na Jihar kaduna, shugaban yan Sanda na kasa da Abubakar Musa Abubakar suka yi na tsare Alhaji Sani Dauda, Alkali Almisri, Shehu Sani Dauda suk an tsare su ba bisa ka’ida ba”, inji Lauya Maxwell.
Lauyan ya kuma ci gaba da cewa kotun ta kuma yanke hukuncin a biya naira miliyan biyu a kan tsarewar da aka yi wa Alhaji Sani Dauda da sauran mutanen da aka tsare ba bisa ka’ida ba.
Shima da yake zantawa da manema labarai Lauyan Abubakar Musa Abubakar Safiyanu Sa’idu Tambai cewa ya yi su ba su gamsu da hukuncin ba don haka za su daukaka kara zuwa kotun gaba, bisa hujjar da ya ce kotun bata yi amfani da abubuwan da aka gabatar gabanta ba duk da sun gabatar mata lokacin da suke gabatar da jawabi da hujjoji a gaban kotun.
Kamar yadda Lauya Tambai ya shaidawa manema labarai cewa ” a bisa yadda suka kalli shari’ar su an ajiye duk hujjojinsu da suka gabatar a gaban kotu an kalli abin da kawai masu kara suka gabatar gabanta saboda a iya saninsu kamar yadda ya ce Alkalin Alkalai ba zai yanke hukunci ba shi a kansa kawai sai kotu ta zauna ko su Alkalin Alkalai tare da alkalai da ake cewa Kadi kadi kamar yadda yake a Shari’ia ba mutum daya kawai ba don haka zamu daukaka kara”, inji Lauya Safiyanu Sa’idu Tambai.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.