Home / Labarai / Ba Mu Goyon Bayan Korar Ma’aikata – Yan Kwadago

Ba Mu Goyon Bayan Korar Ma’aikata – Yan Kwadago

Ba Mu Goyon Bayan Korar Ma’aikata 

Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Suleiman ya bayyana cewa su a matsayinsu na yayan kungiyar kwadago ba su amince da irin yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ke korar ma’aikata.
Kwamared Aliyu Magaji Suleiman ya shaidawa manema labarai hakan ne a wajen babban taron tunawa da ranar Gwagwarmayar ma’aikata ta shekarar 2021 da aka yi a Kaduna.
Ayuba Suleiman, ya ce su a matsayinsu na yayan kungiyar kwadago ba su koyon bayan irin yadda Gwamnati ke kokarin korar ma’aikata, “akwai irin yadda doka ta yi tanajin a Kori ma’aikata don haka dole ne sai an bi tanajin dokar kafin a Sallami  duk wani ma’aikaci, amma yadda lamarin ke tafiya a halin yanzu ba wani ma’aikacin da zai amince da shi wannan tsarin ko kadan”.
Kamar yadda kowa ya Sani dukkan yancin da ma’aikata suka samu babu inda aka same shi daga kwance dole sai da aka tashi a tsarin Gwagwarmaya sannan bukata ta biya.
“Saboda haka ne muka ware nan da bayan Sallah idan Allah ya kaimu za mu kira yajin aiki na kwanaki biyar domin mu nuna bacin ran mu game da wannan batu na korar ma’aikata da ake yi a Jihar Kaduna, kuma koda uwar kungiyar kwadago ta kasa ma za ta fayyace na ta matsayin duk a bayan an kammala Azumi”. Inji kwamared Ayuba Magaji
Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya ci gaba da bayanin cewa kamar yadda kowa ya Sani ba wai ma’aikatan Gwamnati ba ne kawai suka kasance yayan kungiyar kwadago ba, kashi Saba’in na masu aiki a wurare masu zaman kansu duk yayan kungiyar ne kamar yadda aka gani a wajen bikin nan na ranar ma’aikata ta Bana,  don haka kungiyar na yi wa kowa aiki ne domin kasa ta ci gaba.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.