Home / News / Buhari Na Kiran Ayi Noma Ne Domin Ya Taimaki Kasa, Tattalin Arzikin Ta – Tijjani Bambale

Buhari Na Kiran Ayi Noma Ne Domin Ya Taimaki Kasa, Tattalin Arzikin Ta – Tijjani Bambale

Imrana Abdullahi
Wani mai sharhi a kan al’amuran Yau da kullum Alhaji Tijjani Bambale, ya bayyana kiraye Kirayen da shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari ke yi wa manoma na su tashi tsaye domin samar da abinci a kasa da cewa abune wanda ya dace kuma ya nuna irin yadda shugaba Buhari ke kishin kasar da al’ummarta baki daya.
Alhaji Tijjani Bambale ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawar da ya yi da wakilinmu ta manhajar whatsapp, saboda wannan hanya da shugaban kasa ke magana a kanta a tashi ayi Noma itace mai bullewa a gar mu, domin an gina Nijeriya ne tun asali ta hanayar Noma. Ganin an gina Nijeriya da duk wani tattalin arzikin da muke takama da shi tin asali ta hanyar Noma ya zama wajibi mu ci gaba da rike shi. Saboda shi ne mafi alfanu gare mu ko a nan gaba.
Tun fa bamu zama komai ba har a yanzu muka zama komai, kuma makomar tattalin arzikin duniya da a gare mu shi ne mu rike Noman nan shi me mafita gare mu, ta yadda koda an shiga cikin wani hali na tabarbarewar tattalin arziki a duniya mu ba zamu tagayyara ba saboda a kullum kayan abinci sai an neme su a kowane hali aka shiga.
Mutane su duba yanayin da aka shiga a bangaren tattalin arzikin mai , amma idan batun Noma ne waye zai ce batun abinci ya shiga hali a duk duniya dole ne a nemi abinci a kowa ne hali aka shiga domin mutum bai yi sai da abinci.
Kuma shi shugaban kasa na kiraye kirayen ayi Noma me domin ya taimaki kasar da tattalin arzikin ta baki daya.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.