Home / Big News / Cutar Korona Ta Kashe Wani Dan Nijeriya

Cutar Korona Ta Kashe Wani Dan Nijeriya

Bayanan da muke samu na tabbatar da cewa an samu mutum na farko da ya mutu saboda cutar covid 19 da ake kira Korona

Cibiyar kula da yaduwar cututtuka ta Nijeriya ce ta bayyana hakan a ranar Litinin a ssahihin shafinta na tuwita domin sanar da jama’a abin da ya faru game da lamarin.

Kamar yadda hukumar kula da yaduwar cututtukan ta NCDC, ta bayyana cewa wanda ya mutun dan shekaru 67 ne kuma Namiji da ya dawo daga neman lafiya daga kasar Ingila.

Amma bayan dawowarsa sai yanayinsa na lafiya ya zama cikin wani mawuyacin hali

Wannan yanayi ne yasa iyalinsa wato wanda ya kamu da cutar suka fitar da wata sanarwar manema labarai da suka bayyana maralafiyar da sunan Suleiman Achimugu, wanda tsohon Manajan Darakta ne na PPMC.

Sanarwar dai na dauke ne da sa hannun Abubakar Achimugu ta ce wanda ya kamu din na can wani wuri a Kebe tun lokacin da ya dawo daga kasar Ingila kuma an shaidawa hukumar NCDC game da alamun cutar Covid 19 da ake gani a tare da Suleiman Achimugu.

” Muna bakin cikin shaida maku rasuwar uban my abin kaunar mu, dan Uwa Injiniya Suleiman Achimugu tsohon Manajan Darakta a kamfanin PPMC

“Ya rasu sakamakon cutar Covid 19 a ranar 22 ha watan uku, 2020 yan kwanaki bayan ya dawo daga kasar Ingila.

“An Gwada shi an kuma same shi da cutar tuni aka dauke shi zuwa asibitin kwararru, amma ya rasu lokacin da ake duba lafiyarsa a can”.

“muna neman addu’ar Allah ya gafarta masa kuma ya warkar da daukacin marasa lafiyar da suka da cutar”.

Tuni dai aka yi Jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya shimfida.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.