Home / Labarai / Daliban Wasilatul huda Littafizul Kur’an Sun Karrama Bello Kagara

Daliban Wasilatul huda Littafizul Kur’an Sun Karrama Bello Kagara

Daliban Wasilatul huda Littafizul Kur’an Sun Karrama Bello Kagara
Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar yadda zaku iya gani a wannan hoton daliban makarantar Wasilatul huda Littafizul Kur’an sun Karrama Alhaji Bello Kagara, da lambar girmamawa bisa kokari da Kwazon da yake nunawa wajen ciyar da harkokin ilimi da zaman lafiya gaba a dukkan yankin.
Kamar yadda zaku iya gani a wannan hoton yara dalibai sun mika wannan lambar ne a wajen taron Karrama Bello Kagara da aka yi a garin Kagara domin nuna gamsuwa da irin ayyukan alkairin da Alhaji Bello Hussain Kagara ke aiwatarwa domin ciyar da al’umma gaba.
Su dai daliban sun bayyana cewa karramawar sun mika ta ne domin kokarin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da Alhaji Bello Kagara yake kokarin aiwatarwa domin ciyar da al’umma gaba.
Taron karramawar dai da aka yi a filin makarantar Firamare ta Kagara, ya samu halartar dimbin jama’a da suka samu halartar wannan babban taron da suka hada da shugaban hukumar ilimin Firamare ta Jihar Katsina, Daraktan tsangayar ilimi ta jami’ar Ahmadu Bello Zariya da Kwamishinan ilimi na Jihar Katsina Farfesa Badamasi Lawal Charanchi wanda a hoton zaku ganshi ya rike takardar karramawar da aka ba Bello Kagara.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.