Home / Labarai / Dalilin Da Yasa Na Zabi Bamalli Sarkin Zazzau – El- Rufa’i

Dalilin Da Yasa Na Zabi Bamalli Sarkin Zazzau – El- Rufa’i

Imrana Abdullahi

 

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I, ya bayyana nadin sabon Sarkin Zazzau Jakada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sarki na 19 daga tsatson Fulani an yi ne domin Gwamnati ta gyara irin abin da turawan mulkin mallaka suka yi na rashin adalci.

 

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron bayar da Sandar mulki da kuma rantsuwar kama aiki a matsayin sabon Sarkin Zazzau na 19 da aka yi a filin kwallon Dawaki da ke Zariya a ranar Litinin.

 

Kamar yadda ya ce kakan wannan sabon Sarki Aliyu Dan Sidi an yi masa rashin adalci na sauke shi daga kan kadon sarautar Zazzau da turawan mulkin mallaka suka yi na Gwamnatin lardin Arewa suka yi, wanda a wancan lokacin Gwamna Herbert Symonds Goldsmith ke shugabanta.

 

Kamar yadda Gwamna El Rufa’I ya ce wannan mikawa sabon Sarkin Sanda ” ya zo ne a dai dai lokacin da ake cika shekaru 100 tun bayan da tsohon Gwamnan lardin Arewa, Herbert Symonds Goldsmith, ya cire Sarkin Zazzau marigayi Aliyu Dan Sidi daga kan sarautar Zazzau”.

 

Gwamnan ya ci gaba da cewa sakamakon rasuwar marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, ya kasance kujerar Sarkin ba kowa a kanta, hakan ya ba Gwamnati damar yin abin da suka yi.

 

‘’Shehu Usman Dan Fodio a cikin wani littafin da ya rubuta mai suna ‘Bayan Wujub Al-Hijra’ ya bayyana karara cewa da akwai muhimman abubuwa da suke tabbatar da ingancin shugabanci a tsarin musulunci, inda ya lissafa su Dalla Dalla, har suka cika baki daya.

 

Gwamnan ya kuma yi kira ga daukacin Hakimai, mambobin masarautar Zazzau da daukacin al’ummar Jihar Kaduna da su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga sabon Sarkin somin a samu nasarar da ake bukata wajen ciyar da yankin masarautar Zazzau,Jihar Kaduna da kasa baki daya gaba.

 

El Rufai ya kuma mika gargadi cewa ’”Gwamnatinsa na tsammanin samun cikakken hadin kai da goyon baya ga dukkan sarakuna da daukacin masarautunmu kuma idan aka kasa hakika Gwamnati ba za ta yi kasa a Gwiwa ba wajen ganin ta dauki mataki ga dukkan wanda ke neman haifar da sabanin abin da yakamata ga sarauta musamman masarautar Zazzau”.

 

‘’ A shekaru 45 na masarautar Zazzau da marigayi ya kwashe ana bayyana marigayin a matsayin wani mutum kaifi daya da ke son tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jama’a abin da ya tabbatar da shi matsayin Uba ga kowa.

 

“shawara a matsayin Uba musamman a wajen taron da muke yi a duk sati zai ci gaba da kasancewa a cikin zukatanmu.Allah ya jikansa ya gafarta masa yasa Aljanna ta zama makomarsa”, El- Rufa’I ya bayyana.

 

Gwamnan ya bayyana cewa hakika yana da kwarin gwiwa a game da sabon Sarkin Zazzau Bamalli “zai iya gabatar da wannan aiki na shugabantar jama’a a matsayin Sarkin Zazzau na Goma sha tara domin ginawa a kan inda sauran sarakunan kasar Zazzau suka Dora, ya kara da cewa irin kokarin da kake yi domin ganin ci gaban kasar Zazzau tare da al’ummarta ya dace a ci gaba.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.