Home / News / Dan Majalisa Salisu Iro Isansi Ya Rabawa Mutane 1000 Tallafi A Katsina

Dan Majalisa Salisu Iro Isansi Ya Rabawa Mutane 1000 Tallafi A Katsina

Daga Surajo Yandaki Katsina
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya Honarabul  Salisu Iro Isansi, ya bada tallafin dubu goma, ga mutane (10,000)domin su inganta  kananan sana’o’i da suka hada da mutane  dubu (1000) mata da matasa na cikin mazabarsa
“A jawabinsa na maraba Dan majalisa  Salisu Iro Isansi ya ce ya bada wannan tallafin don rage radadi ga Al’ummar mazabarsa, bada tallafin zai taimaka wajen habbaka kananan sana’o’in al’ummar mu, musamman irin wannan yanayi da ake ciki na karayar tattalin arzikin wanda ya shafi duniya baki daya ba Nigeria ko jihar Katsina kawai ba.
Mun bada wannan tallafi ne karkashin hukumar kula da masu kananan sana’o’i ta kasa (SMEDAN). Don isar da tallafin ga masu kananan sana’o’in.
“Da yake gabatar jawabin sa, a wurin taron shugaban hukumar kulada masu kananan sana’o’i ta kasa (SMEDAN)  Dakta Dikko Umar Radda ya bayyana cewa Dan majalisar cikin kudin shi da ake bashi na hidimar majalisa (alawus, alawus) ya bada karkashin  hukumar da nike jagoranta (SMEDAN) babu ko kobo daya fito daga hukuma ta. Ya bamu don rabasu inda yakamata.
Wannan ba karamin kokari bane Dan majalisar ya yi, yakamata, a yaba masa”. “Inji Dikko Umar Radda”.
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, wanda kwamishinan ma’aikatar Ruwa Alhaji  Musa Adamu FUNTUA ya wakilta Kwamishinan Ruwan ya jinjina ma Dan majalisar kan wannan kokari da ya yi.
Wannan abin ayaba ne, bada tallafin dubu goma, goma ga mutum dubu ba karamin al’amari bane. “Ya cigaba da cewa yaga kokarin Hon. Salisu Iro Isansi dabai rude ba, matsayin shi na mai wakiltar wannan babbar mazaba, Allah ya karkato da hankali shi wajen aikata abin alheri mai girma irin wannan, kuma a mazaba ta babbar binnin jiha mai yawan jama’a”.
“Shima a nashi jawabin uban kasa Magajin Garin Katsina Alh. Aminu Abdulmuminu Kabir Usman wanda ya samu wakilcin wakilin kudun katsina Alh. Abdu Ilyasu ya bayyana cewa matsayin mu na uwayen Al’umma munji dadin wannan abun alherin da Dan majalisa Hon. Salisu Iro Isansi ya bada Al’ummar wannan mazaba tamu. “Daga Karshe wakilin kudun ya jawo hankalin Dan majalisar daya cigaba da irin wadannan ayyukan alherin ga Al’umma don taimaka ma tattalin arzikin su. “Rashin abun yi ko sana’a tsakanin matasan mu yana daya daga cikin abinda ke kawo barazana ga harkar tsaron jihar nan da kasar nan baki daya”.
Taron ya samu halartar Mai girma Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari wanda ya samu wakilcin Kwamishinan ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta jihar Katsina Hon. Musa Adamu FUNTUA, Shugaban hukumar kulada masu kananan sana’o’i ta kasa (SMEDAN) Hon. Dr. Dikko Umar Radda, Hon. Aliyu Abubakar Albaba Dan majalisa jiha mai wakiltar karamar hukumar Katsina, Shugaban jam’iyyar Apc na karamar hukumar Katsina Alh. Babangida Shinkafi.
Sauran sun hada da Dr. Babangida Abubakar Albaba shugaban makarantar koyon ilmin na’ura mai kwakwalwa, kimiyya da fasaha da kere, kere, Haj. Amina Lawal Dauda Mani Maiba Gwamna shawara kan Ilmin Yaya mata, Elder Alh. Ali Guguwa, shugabannin jam’iyyar Apc na mazabun karamar hukumar Katsina goma sha sun halarci wannan taro.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.