Home / Lafiya / Dana Ya Kamu Da Cutar Korona Birus – Atiku

Dana Ya Kamu Da Cutar Korona Birus – Atiku

TSOHON mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce dansa na cikinsa ya kamu da korona Birus

Atiku Abubakar, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twiiter.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce tuni aka kai dan nasa asibitin koyarwa da ke Gwagwalada a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya inda ake masa magani.

Atiku Abubakar ya bukaci al’umma da su saka dan nasa a cikin  addu’a.

Ya zuwa yanzu dai a hukumance akwai mutum 30 da suka kamu da cutar korona Birus wato ( Covid 19) a Najeriya, idan aka hada da dan Atiku kuma adadin zai kai 31 kodayake hukumar takaita yaduwar cutuka ta kasar ba ta sanar da na dan Atikun ba.

Mutanen da ke dauke da annobar korona Birus a nahiyar Afirka sun zarce mutum 1,000 a karshen wannan makon kamar yadda hukumar da ke yaki da cututtuka ta nahiyar ta bayyana.

Kasar Uganda ta bayyana mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar inda kasar ta ce wani fasinja ne da ya zo daga Dubai.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.