Home / Health / Dole A Dauki Matakin Salwantar Rayuka A Kan Titunan Nijeriya – Issa Aremu

Dole A Dauki Matakin Salwantar Rayuka A Kan Titunan Nijeriya – Issa Aremu

Daga Imrana A Kaduna
An Bayyana matsalar salwantar rayuka sakamakon hadurra da ake samu kan titunan Nijeriya a matsayin illar da wuce cutar sida ko kanjamau da makarantansu.
Kwamared Issa Aremu ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyyar mutuwar tsohon sakataren kungiyar yan jaridu reshen jihar kaduna kwamared Dominic Uzu a sakatariyar da ke cikin garin kaduna.
Kwamared Issa Aremu ya bayyana cewa hakika matsalar salwantar rayuka ta hanyar hadarin mota a fadin kasar ya zama wani al’amarin da ke bukatar kowa ya tashi tsaye domin matsalar ta zama tamkar ta’addaci ne a tsakanin da yake bukatar a kawar da lamarin baki daya.
Aremu ya bayyana cewa an yi babban  rashi bisa ga irin yadda marigayin ya bayar da gudunmawarsa a bangaren aikin jarida ta hanyar fadakarwa da wayar da jama’a da muhimman bayanan da ya dace a sani, ha shi kuma ya yi ma’ajin kungiyar yan jarida reshen Jihar kaduna ya kuma yi sakataren kungiyar na Jiha baki daya.
Ya ci gaba da cewa ya zama dole a kawo karshen wannan lamari baki dayansa da ya zama wata cuta mai kama da karfanfana da ke neman likewa kowa.
Issa Aremu ya jajantawa daukacin yayan kungiyar baki daya game da lamarin da ya faru a ranar Talata 4 ga watan Fabrairu, 2020 kan hanyar kaduna zuwa Zariya sakamakon wani mummunan hadarin mota.
Ya bayyana mutuwar Domnic Uzu a matsayin wani babban rashi ga yayan kungiyar na kasa da kuma iyalai, hakika zamu ci gaba da irin yadda ya kawowa kungiyar ci gaba tun daga matakin Jiha zuwa kasa baki daya.
 Aremu ya kara ankarar da daukacin jama’a inda ya ce babbar hanyar da zamu yi makokin marigayi kwamared Domnic Uzu shi ne ta hanyar hada hannu tare domin ganin karshen faruwar hadurra irin wannan a tsakanin al’umma kasancewar rayuka na tafiya haka kawai a kan titunan Nijeriya, a don haka ya yi kiran cewa akwai bukatar a ci gaba da gina titunan
“Hawaye kawai ba za su Isa ba balantana yin kuka zuci ko a boye dole a lalubo hanyoyin magance matsalar musamman ganin cewa wadansu direbobin na yin gudu fiye da ka’idar yin tuki  wasu kuma na haifar da hadarin ne sakamakon kokarin kaucewa ramukan kan hanya ga kuma masu tukin ganganci da sauran dalilai da dama.
Ya ci gaba da cewa wadanda hadarin salwantar rayukan jama’a ya fi shafa a mafi yawan lakuta su ne Iyaye maza da mata da kuma yayan da ake mutuwa ana barinsu sakamakon hadarin mota.
Ya dace mu diana kallon batun hadarin mota da cewa lamari ne na samar da cikakkun alkalumman wadanda suka rasa rayukan nasu, don haka sai mu canza tunani don ganin kwamared Domnic Uzu ya mutu ya bar mata daya da yaya hudu da kuma yan uwa da dama tare da abokan aiki da abokan arziki baki daya.
“Kamar yadda alkalumman kididdiga ke nunawa shi ne faruwar hadarin mota na lakume rayuka kamar yadda batun ta’addanci ke lakumewa a cikin al’umma, don haka mutuwar wannan dan jaridar Domnic Uzu ya zama wata manuniyar tashi tsaye ayi yaki da matsalar hadurra a lan titunan Nijeriya saboda illar da lamarin ke haifarwa”.
Ya ci gaba da bayani a cikin takardar da Issa Aremu Janaral Sakatare na kungiyar ma’aikatan masaku ta kasa kuma dan majalisar kolin kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC sannan mataimakin shugaban kungiyar masana’antu ta duniya, ya tabbatar da wadansu alkalumman da ke bayanin cewa ana samun salwantar rayukan jama’a sama da dubu 39, 000 a kowace shekara a Nijeriya sannan hukumar kula da harkokin lafiya ta majalisar dinkin duniya (WHO) a wani rahoton da ta fitar a shekarar 2018 ta fitar da alkalumman da ke cewa ana samun munanan hadurra  a Nijeriya da suka kai dubu 39,802 yayin da aka kiyasta ha dukkan yawan mutane dubu 100,000 salwantar rayukan da ake samu ya kai kashi 21.4 a Nijeriya wanda ya tabbatar da cewa Nijeriya na rasa jama’a fiye da kasashen Guinea, Liberiya da Saliyau da ya kai dubu 11,310 sakamakon matsalar cutar Ebola.
Don haka muna kira ga maza da mata da lallai a tashi tsaye domin magance salwantar rayuka ta hanyar hadarin mota da muke samu a kan titunan Nijeriya.
Domin kamar yadda wani jami’in hukumar kula da matsalar hadarin Nijeriya ya bayyana mai suna Abubakar Murabus Tata, cewa hadarin da ya kashe Domnic ya faru ne sakamakon hadarin da ya rutsa da wasu motoci biyu babbar mota kirar DAF da kuma motar Toyota Bus ta haya da kuma rashin kyawun hanya saboda ramuka don haka mafi yawan hanyoyi ba su da dadin tafiya sannan kuma direbobi na tukin ganganci duk da jami’an hukumar na kan hanya.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.