Home / KUNGIYOYI / Gamayyar Kungiyoyin Funtuwa Sun Koka Game Da Wutar Lantarki

Gamayyar Kungiyoyin Funtuwa Sun Koka Game Da Wutar Lantarki

Gamayyar Kungiyoyi da ke Funtua, wanda suka hada da Funtua Consultative Forum, FUNYUD, Funtua Huntun Dutse, a karkashin jagorancin shugaban makarantar Muslim Community College of Health Sciences and Technology da ke Funtuwa suka kai ziyara ofishin Shiyya na Kamfanin da ke rarraba Wuta na Funtua watau KEDCO, Funtua Regional Office.

 

Da nufin tattaunawa ta yadda za a shawo kan matsalar Wuta lantarki a Funtua da kewaye.

Wakilan wadannan Kungiyoyin sun sami tattaunawa da Shuwagabannin shiyar Funtua, kuma cikin ikon Allah an samu matsaya kan koken al’umar wannan Yanki namu mai albarka.

Shuwagabannin KEDCO sun tabbatar mana da cewa za’a kara awowi na Samar da wuta, tare da kawo babbar na’urar rarraba wutar lantarki mai karfin  15MVA,  don magance rashin issar wutar lantarki a Funtua da kewaye.

 

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da sakatariyar kwamitin yada labarai ta kungiyar tuntuba domin ci gaban Funtuwa (FCF) Maryam Abubakar ta sanyawa hannu aka rabawa manema labarai, domin bayyana wa hukumomi da al’ummar duniya halin da ake ciki a Funtuwa game da tsananin karancin wutar lantarki a Funtuwa da kewaye kamar yadda yake a rubuce a cikin takardar.

Haka kuma an tattauna yadda za’a rage yawan kudaden da ake cajin Jama’a a estimated bills.

A Watannin baya kungiyar tuntuba ta (Funtua Consultative Forum)  ta yi  kokarin ganin an shawo kan matsalar Wuta lantarki a Funtua.

Saboda haka ana saran Yanzu da wannan Gamayyar kungiyoyi ana  sa ran matsalar Wuta lantarki za ta zama tarihi a Funtua, da ikon Allah.

Gamayyar kungiyoyin sun yi fatan  alkairi  tare da yin addu’ar  samun isassar wutar lantarki domin  ci gaban Funtua da kewaye.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.