Home / KUNGIYOYI / Gwamna Zulum Ya Kai Ziyara Ofishin Tarayyar Turai, Ya Bukaci Ayi Aiki Da Yan Kwangilar Nijeriya

Gwamna Zulum Ya Kai Ziyara Ofishin Tarayyar Turai, Ya Bukaci Ayi Aiki Da Yan Kwangilar Nijeriya

Gwamna Zulum Ya Kai Ziyara Ofishin Tarayyar Turai, Ya Bukaci Ayi Aiki Da Yan Kwangilar Nijeriya
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum a yau ranar Alhamis ya kai ziyara ga sabuwar shugabar da ke jagorantar aikin kungiyar tarayyar Turai a Nijeriya, Misis Cecile Tassin- Pelzer.
Zulum, a lokacin ziyarar da ya kai gidan na tarayyar Turai ya bukaci da a rika yin amfani da yan kwangilar mu na gida musamman a lokacin yin ayyukan da za a yi a Borno.
Gwamnan ya kuma bukaci da a yi kari a kan wadansu ayyukan ci gaban da ake yi a Jihar, inda ya yi godiya tare da jinjina ga kungiyar tarayyar Turan bisa taimakon da suke bayarwa.
Sai dai Gwamna Zulum ya yi jan hankali game da batun yin aiki da gaskiya da kuma rikon Amana wajen aiwatar da dukkan aiki.
Gwamnan ya kuma yi wa sabuwar shugabar marhabin da maraba da zuwa Nijeriya, inda ya yi mata albishir da samun dukkan hadin kai da goyon baya.
“Tun lokacin da nake aiki a matsayin kwamishina, ina da kyakkyawar alakar aiki da kungiyar tarayyar Turai. Don haka ne na zo domin in yi maki murna da kuma marhabin da zuwa Nijeriya”, Inji Zulum.
Zulum ya kuma yabawa Mista Kurt Cornelis bisa irin yadda ya gudanar da aiki tare da samar da kyakkyawar dangantaka a tsakanin bangarorin biyu.
Gwamnan ya samu Rakiyar mai bashi shawara ta musamman kuma kodinetar shirin SDG, Dokta Mairo Mandara.
Da take mayar da jawabi, Misis Tassin – Pelzer ta bayar da tabbacin yin aiki tare cikin kyakkyawan yanayi da Gwamnatin Jihar Borno.
Ta kuma bayar da tabbaci ga Gwamnan cewa har yanzu ana daukar Nijeriya a matsayin kasa ta musamman a batun ayyukan jin kai da suke yi.
Misis Tassin-Pelzer ta yi aiki tsawon shekaru uku a Senegal kafin a kawo ta Nijeriya.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.