Home / Labarai / Gwamna Zulum Ya Lashi Takobin Gyara Tashar Lantarkin TCN

Gwamna Zulum Ya Lashi Takobin Gyara Tashar Lantarkin TCN

Gwamna Zulum Ya Lashi Takobin Gyara Tashar Lantarkin TCN
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya lashi Takobin ganin ya gyara tashar rarraba wutar lantarki domin taimakawa hukumar raba wutar lantarki ta kasa.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ne a ranar Juma’a wurin tashar samar da wutar lantarkin da Yan Boko Haram suka lalata, wanda sanadiyyar hakan ya haifar da matsalar samar da hasken lantarki  a Maiduguri da kuma wani bangare na karamar hukumar Jere.
Ita dai wannan tashar wutar lantarkin na kan babban titin Maduguri zuwa Damaturu ne babban birnin Jihar Yobe.
Ziyarar da Gwamnan ya kai na da nufin taimakawa hukumar samar da wuta tare da rarraba wa jama’a domin su samu damar dawowa da babban birnin Maiduguri da kewaye da wutar lantarkin.
Harin da aka kaiwa Tashar a kwanan ne shi ne karo na uku da yan Ta’adda suka yi wanda sanadiyyar hakan ya Jefa daukacin birnin cikin Duhu.
Wannan matsalar rashin samun wutar dai ta faru ne tsawon sama da kwanaki Bakwai lamarin da ya haifar da durkushewar harkokin kasuwancin musamman ga wadanda suka dogara da wutar lantarkin.
Da yake tofa albarkacin bakinsa game da ziyarar da Gwamnan ya kai wurin da ake aikin gyaran, Injiniyan kamfanin samar da wutar tare da taimakon ma’aikatar Gidaje da samar da lantarki na  Jihar suna yin aiki tukuru domin ganin an warware matsalar baki daya domin wutar lantarki da samu a Maiduguri.
Gwamnan ya bayyana cewa tuni aka dauki matakin wuccin gadi domin dawowa da birnin na Maiduguri wutar lantarki, yayin da Gwamnati za ta yi aikin hadin Gwiwa ta kamfanin samar da wutar lantarki na kasa domin warware matsalar kacokam baki daya kowa ya huta.
“Kunga irin yadda matsayin lalacewar ya kai  sun yi amfani da abubuwan fashewa ne suka fasa wurin. Don haka ne muka zo domin ganewa idanuwanmu yadda abin ya faru da kanmu,wanda cikin ikon Allah ya mu hanzarta gyara dukkan abin da suka lalata”, Inji Zulum.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.