Home / Big News / Gwamnatin El – Rufa’i, ta mayar da Dokar Hana Fita Ranakun Laraba Da Alhamis

Gwamnatin El – Rufa’i, ta mayar da Dokar Hana Fita Ranakun Laraba Da Alhamis

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kara matsar da dokar hana fita ta kwanaki biyu daga ranakun Laraba da Alhamis, wannan matakin kamar yadda wata sanarwa ta bayyana sun yi hakan me domin bayar da dama ga jama’a su ziyarci Kasuwannin unguwanni su sayi kayan abinci da sauran kayan masarufi.

A cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun Manajan Daraktan bunkasa Kasuwannin Jihar Kaduna Muhammd Hafiz Bayero, da ya fitar a ranar Lahadi, ta ce ranakun Laraba da Alhamis ne ranakun da aka amince su fita domin sayen kayan abinci da magani da dai kayan masarufi saboda sassauta dokar hana fita a Jihar.

” Mutane na da damar ziyarar Kasuwannin unguwanni a ranakun 20 da 21 na watan Mayu , 2020 domin sayen kayan abinci da sauransu., wannan na nufin cewa babu wata kasuwar da za a bude a ranar Asabar”, Ya tabbatar.

Muhammad ya kumankara jaddada cewa Kasuwannin na unguwanni za su kasance a bude ne daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na Yamma sakamakon sassauta dokar.

Kamfanin kasuwar ya bukaci jama’a da su ci gaba da kiyaye doka da oda tare da tanaje tanajen Sanya abin rufe hanci da baki da kuma bayar da hadin kai domin duba mutane na wuccin gadi lokacin shiga Kasuwannin unguwannin sai kuma bayar da tazara da dai sauran ka’idojin kula da lafiya.

Manajan Daraktan ya kuma bayar da tabbacin cewa an yi dukkan tanaje tanajen da suka kamata domin taron dukiya da lafiyar jama’a a Kasuwannin wuccin gadin da aka tanadar

Sanarwar ta kuma jinjinawa irin yadda masu cin kasuwar suke gudanar da harkokinsu a Kasuwannin unguwanni na wuccin gadi domin a Kasuwannin unguwannin guda 40 zuwa 46 harkoki sun ta fi daidai kamar yadda ya dace

‘’ Da wannan ne Kamfanin kasuwar kaduna ke kara fadakar da masu kokarin mayar da titunan kusa da kasuwa ya zuwa wadansu shagunan da suka kasance haramtattu me ” , inji sanarwar.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.