Home / News / Hassan Hyat Da Ibrahim Wusono Sun Lashe Zaben Shugabancin PDP A Kaduna

Hassan Hyat Da Ibrahim Wusono Sun Lashe Zaben Shugabancin PDP A Kaduna

Hassan Hyat Da Ibrahim Wusono Sun Lashe Zaben Shugabancin PDP A Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi

Bayanan da muke samu daga Ofishin jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna na cewa tsohon ministan harkokin sufurin Jiragen sama Honarabul Felix Hassan Hyat ya sake lashe zaben shugaban Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna, domin jagorancin wadansu shekaru hudu masu zuwa.

Daga cikin wadanda suka samu nasarar dawowa a matsayin zababbu sun hada da Honarabul Ibrahim Lawal Nuhu, a matsayin mataimakin shugaba, Honarabul Ibrahim Aliyu Wusono, Sakatare na Jiha, Honarabul Abdullahi Rilwanu Sakataren kudi.

Sai Honarabul Magaji Ahmed Jarma, Sakataren tsare tsare, Musa Gaga Kukui, mai binciken kudi, Honarabul Abraham A. Catch, Sakataren yada labarai na Jam’iyyar, Honarabul Murna S. Amboson shugabar mata ta Jiha, Honarabul Aliyu Bello shugaban Matasa da Barista Ibrahim Khalid mai bayar da shawara a kan harkokin shari’a.

A taron da aka yi tsawon kwanaki biyu domin zaben shugabannin jam’iyyar na kwanaki biyu a babban dakin taron kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna, inda aka tace kuri’un mutanen da ya dace su Jefa kuri’a da duka kai dubu 2655, Honarabul Hassan Hyat ya samu nasarar lashe kuri’u 1907 wanda ya bashi damar kayar da abokin takararsa Ashafa Waziri, da ya samu yawan kuri’u 471 dai dai.

 

Yayin da Sakataren Jam’iyyar Ibrahim Aliyu Wusono ya samu kuri’u 1779 da samu nasarar kayar da abokin karawarsa Bashir Aliyu (Majoriti) da ya samu kuri’u dari 320.

Shugaban kwamitin gudanar da zaben Cif Ramon Dabo, da ya kula da zaben ya sanar da Honarabul Hyat a matsayin wanda ya lashe zaben kuma ya dawo a matsayin zababben shugaba kasancewarsa ya cika dukkan Sharuddan zabe tare da samun kuri’un da suka fi na kowa yawa.

Dabo, ya godewa wadanda suka gudanar da zaben irin yadda suka gudanar da zaben musamman kafin ayi zaben da lokacin zaben da bayan zaben

A jawabinsa bayan an sanar da shi ya lashe zaben Honarabul Hassan Hyat shima ya yi godiya ga wadanda suka yi zaben musamman irin yadda suka ga dacewarsa ya ci gaba da shugabancin jam’iyyar na wadansu shekaru hudu masu zuwa.

“Ina taya dukkan wadanda suka lashe zaben murna da dukkan wadanda suka shiga takarar zabe a kowane irin mataki, don haka ina kira ga dukkan yayan jam’iyya da jama’ar Jihar Kaduna da su shirya kokarin karbar mulkin Jihar Kaduna”.

Shugaban kwamitin rikon jam’iyyar Barista Bashir Tanimu Dutsinma godiya ya yi ga daukacin yayan jam’iyyar lokacin da yake mika ragamar shugabanci ga sabon shugaban jam’iyyar.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.