Home / Labarai / Jirgin Kasa Ya Yi Hadari A Kaduna

Jirgin Kasa Ya Yi Hadari A Kaduna

 

Imrana Abdullahi

Sakamakon matsalar sace madaurai  da Takalman da ke rike da karafunan titin Jirgin kasa a dai dai unguwar Kanawa cikin garin Kaduna ya haifar da watsewar Taragon Jirgi guda hudu daga cikin sha biyar na kayan bututun ruwa da Jirgin ya dauko daga Tashar Jirgin ruwan Apapa Legas zuwa Saye a birnin Zariya.
Kamar yadda shugaban shiyya na tashar Jirgin kasa Yarima Isma’il Adebiyi ya shaidawa manema labarai a wurin da hadarin ya faru cewa wannan shi ne sawun na biyar da suka dauko na kayan bututun ruwan da suke kaiwa Saye a Zariya cikin Jihar Kaduna.
Isma’il ya ce daman can akwai tsarin da ake da shi na za a yi wa dukkan wuraren da ake Daura kusoshin da ke daure titin Jirgin Kankare da nufin yin maganin masu sace kayan titin Jirgin.
“Muna kira ga iyaye da daukacin jama’a da su yi wa yayansu magana su ja masu kunne a kan irin yadda suke kokarin lalata titin jirgi, kamar yadda wannan hadari ya faru a cikin garin Kaduna ne kuma duk ua faru ne sakamakon matsalar sace sacen kayan titin Jirgin kasa ne da wasu ke sacewa su kaiwa wani mutum a can wani wuri a sayar masa a kudi kadan”.
Ya kara da cewa mutanen Arewa su na da kokarin yin amfani da Jirgin kasa ta fuskar daukar mutane.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.