Home / Labarai / Karfin Bindiga Ba Zai Magance Matsalar Tsaron Nijeriya Ba – Bayero Fullo

Karfin Bindiga Ba Zai Magance Matsalar Tsaron Nijeriya Ba – Bayero Fullo

Karfin Bindiga Ba Zai Magance Matsalar Tsaron Nijeriya Ba – Bayero Fullo
Mustapha Imrana Abdullahi
Sakataren kungiyar matasan Fulani ta FUSADAN Bala Bayero Fullo ya bayyana cewa ba za a samu magance matsalar tsaron da ke faruwa a Nijeriya ba da karfin bindiga ba.
Bala Bayero Fullo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna jim kadan bayan kammala wani taron bitar wayarwa da jama’a kai game da sanin dalilai da abin da ya kawo matsalolin da suke faruwa a Nijeriya musamman a bangaren Fulani makiyaya.
Bala Bayero ya ci gaba da cewa dole ne sai an kira al’umma waje daya musamman Sarakuna da kuma jami’an tsaro domin lalubo meke faruwa tun da farko kuma me ya haifar da wannan matsalar da nufin warware ta baki daya.
Ya kara da cewa ana samun lokutan da ake kama masu mutane wato Fulani kenan haka kawai a karbi abin hannunsu ba su ji ba ba su gani ba kuma ba tare da sun yi wa kowa laifi ba kuma a matsayinsu na yan kasa, dole ya lalubo wannan da nufin magance lamarin kuma hukunta wadanda aka samu da laifi.
A game da dalilin da yasa suka kafa wannan kungiya ta matasan Fulani ta FUSADAN kuwa shi ne domin wayarwa da Fulani baki daya kai a fannonin Ilimin addini da na Boko, “wanda hakika mun lura akwai bukatar hakan kwarai.
“Mu Fulani masu son zaman lafiya ne a koda yaushe a kowane irin lokaci, don haka suke fafutukar jama’a su fahimci hakan.
“Mun kuma gano ana neman haifar da rikici me domin a dagula yankin arewacin Nijeriya baki daya, kuma hakan na zai faru ba da ikon Allah saboda muna da yakinin Allah zai tona asirin masu wannan mugun aiki”.
Ya ce yakamata a Sani cewa ba wai duk Bafulatani bane batagari don haka a daina yi wa Fulani kudin Goro, saboda kamar yadda kowa ya Sani ne babu kabilar da bata da batagari a cikinta don haka ya dace a rika yi wa Fulani adalci a duk lokacin da ake son yin magana game da Fulani.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.