Home / Kasuwanci / Kiwon Kifi Zai Yi Maganin Talauci A Kasa – Ade Tunji Dr Fish

Kiwon Kifi Zai Yi Maganin Talauci A Kasa – Ade Tunji Dr Fish

Mista Ade Tunji da ake yi wa lakabi da ( Likitan Kifi) wato masanin harkokin kiwon Kifi ya bayyana harkar kiwon kifi a matsayin lamari na yake talauci a kowane lokaci kuma a duk fadin duniya baki daya.

Ade Tunji ya bayyana cewa Nijeriya za ta iya dogaro da batun harkar kiwon Kifi ya zama ta yi kafada da kafada da kowace kasa a fadin duniya.

Ade Tunji ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.

Ya ce kamar yadda yake a tsarin kasa cewa zaka iya yin Noma kuma kowane dan kasa zai taimaki Gwamnati ta hanyar taimakon kasa da irin aiyukan sana’a sa yake yi .

Ade Tunji ya ci gaba da bayanin cewa yazo Kaduna ne domin Koyar da jama’a Maza da Mata irin yadda za su yi amfani da harkar Kifi su dogara da kansu, tun daga yadda za su samar da yayan kifi wato yadda za su rika yin Kwankwasa da kuma kiwon kifin baki daya.

” Da irin yadda muke kokarin Koyar da jama’a yadda ake kiwon Kifi ya bayyana a fili cewa lamarin kiwon kifi zai dore a Nijeriya, shi yasa muke fadakar da matasa cewa harkace da za ta taimaka masu har su samu kudi masu yawa”, inji ade tunji.

Ya kara da tabbatar da cewa ku dubi abin da nake rike da shi a hannuna Kifi ne da aka kiwata za a iya sayar da shi sama da naira dubu daya, kuma zai samawa mutum da iyalinsa hanyar abin yi ba tare da samun damuwa ba.

Ya kara da bayanin cewa yana kokarin ganin an samu kasuwa mai inganci da za ta taimakawa masu sana’ar kiwon kifi a Jihar Kaduna da suka kai a kalla mutane dari 200 su samu damar sayar da Kifinsu a kan farashin da ya dace ba kamar yadda lamarin yake a halin yanzu na, misali idan ana sayar da Lemun kwalba na Koka – Kola duk inda ka je a cikin kasa farashin duk daya ne.

Da irin wannan tsarin zamu iya maganin matsalar wasu su rika cutar da wasu masu kiwon kifi.

“Harkar kiwon kifi zai taimaka a kawar da talauci a samu abin yi da kudi kuma a samu abinci kamar yadda ake samu a nama da yake a ko’ina a kasa baki daya, shi yasa nake kokarin kiwon

Koyar da kiwon kifi irin na Tarwada da Karfasa nake yi wa jama’a domin kasa ta amfana.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.