Home / News / Kungiya JESA ta horar da mata da matasa hanyar dogaro da kai

Kungiya JESA ta horar da mata da matasa hanyar dogaro da kai

An kammala horar da mata da matasa 50 yadda za su kasance masu dogaro da kansu ta hanyar koya musu yadda ake sarrafa kayan cimaka da suka hada da Kek da Samosa da shawarma da man abinci (food salad) da sauran girke-gike.

Horon, wanda kungiyar daliban manyan makarantun gaba da sakandiri ‘yan asalin Masarautar Jama’a (JESA) suka gudanar a garin Kafanchan da ke jihar Kaduna, an shiryawa mata ne don koya musu yadda za su zamo masu dogaro da kansu don rufawa kansu asiri da na iyalansu nan gaba.

Yayinda yake jawabi a wajen kammala taron, tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Jama’a, Alhaji Isiyaka Abdullahi Ladan ya hori matasa musamman mata da su tashi tsaye wajen koyon sana’o’i da suka hada da dinki da kwalliya da saka da kayayyakin cimaka da girke-girke na zamani domin a cewarsa, lokaci ne yanzu da maza ke duba irin aikin hannun da mace ta iya kafin ya aureta saboda zamani ne na cude ni in cude ka, ba wai duba kyawun halittar mace ba da galibi baya karko.

Alhaji Isiyaka ya kara da cewa idan har al’umma ta rasa wasu a cikinta da za su tsarawa mata yadda gobensu zai kasance ba, to babu makawa wannan al’ummar tayi matukar asara.

Shima a nasa jawabin, babban bako mai jawabi kuma daya daga cikin wadanda suka assasa kungiyar shekaru da suka wuce, Jamilu Ado Bala, yace duk irin matakin karatun da mutum zai yi a rayuwa idan bai haxa da wani aikin hannu ko wata sana’a ba to ya yiwa kansa babban gibin da sai nan gaba zai yi da na sani.

Bala, ya ce a halin da duniya ke ciki da kuma inda ta fuskanta nan gaba yana nuna mafita kawai ga mutum shine koyon aikin dogaro da kai, inda yayi kira ga matasa da su cire girman kai su kama sana’o’i manya da kanana da za su dogara da shi komai juyin da duniya zata samar don rufawa kansu asiri.

Shugaban kungiyar daliban da ta shirya koyar da sana’ar, Muhammad Sani Adamu, yayi kira ga wadanda suka ci gajiyar da su yi amfani da wannan damar wajen samarwa da kansu hanyar dogaro da kai wajen taimakawa Kansu da ‘yan uwansu da kuma iyalansu a nan gaba ta hanyar koya musu abinda za su rike kansu da shi.

Sannan ya bayyana shirin da kungiyar ke da shi na ci gaba da gudanar da horon a kowace shekara da kuma fito da wasu sabbin shirye-shiryen da za su taimakawa al’umma musamman matasan yankin na karamar hukumar Jama’a.

Mai Martaba Sarkin Jama’a Alhaji (Dr) Muhammad Isa Muhammad II wanda Danmadamin Jama’a Alhaji Aminu Isa Muhammad ya wakilta a ranar budewa, sannan Madakin Jama’a kuma Hakimin Fada, Alhaji Audi Isa Muhammad ya wakilta a ranar rufewa, ya yabawa kungiyar bisa bullo da irin wannan ayyukan don taimakawa jama’ar masarautarsa, inda yayi fatan alheri tare da yin kira ga wadanda suna kammala samun horon da su rike sana’ar da muhimmanci.

A karshe an raba takardun shaidar kammala samun horon ga wadanda su kayi nasarar koyon kayayyakin cimakan da aka koya musu na tsawon kwana tara.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.