Home / Labarai / Lamarin Tsaro Na Kara Tabarbarewa A Arewa – Solomon Dalung

Lamarin Tsaro Na Kara Tabarbarewa A Arewa – Solomon Dalung

Mustapha Imrana Abdullahi
Tsohon ministan Wasanni Barista Solomon Dalung ya koka game da irin matsalar tsaron da ke addabar arewacin Nijeriya wanda sakamakon hakan ake kara samun tabarbarewar al’amura.
Solomon Dalung ya bayyana hakan ne lokacin da ya kaiwa Shaikh Dahiru Usman Bauchi Ziyarar da ya saba kaiwa a duk watan Azumi domin karfafa Dankon zumunci a tsakanin al’ummar musulmi da Kirista.
A wajen taron bude bakin ne da aka ci aka sha tare da tawagar yan uwa mabiya addinin Kirista a cikin gidan Shaihin Malamin, an dai fadakar da Gwamnati da al’umma baki daya a kan bukatar da ke akwai na kowane bangare ya tashi tsaye domin samar da zaman lafiya.
Kasancewa a halin yanzu lamarin tsaro na kara shiga wani mawuyacin hali, shi yasa muke kira da babbar murya a hanzarta daukar matakan gaggawa domin kawo karshen lamarin.
Ya ci gaba da bayanin cewa “hakika a bisa zance mabayyani babu wani mutumin da ya dace ya ceto mu daga wannan yanayin matsalar tsaron da ake ciki da ya wuce kai, saboda babu wanda zaka kira ba zai ji maganarka ba saboda ka taimaka a kasar nan ta fuskokin da dama, ka taimaka dukkan wanda zaka yi wa magana ka yi masa a samu jama’ar kasar nan ta hadu wuri daya a samu ci gaban da ake bukata.
Hadin kai da taimakon Juna shi ake bukata a halin da ake ciki a tarayyar Nijeriya don ba wai batun Gwannati kawai ba ne ita kadai.
Muna kira ga daukacin al’ummar kasa baki daya da su natsu kowa ya rungumi batun zaman tare a guji neman rarrabewa domin babu amfani a cikin rarraba ko kadan.
Da yake nasa jawabin Shaikh Dahiru Usman Bauchi, bayan ya bayyana irin lamarin da ya faru tsakanin musulmi da Kirista a lokacin Najashi inda ya taimakawa musulmi ya boye su kada komai ya same su wanda hakan ya ba al’ummar musulmi da Kirista damar yin ko yi da abin da ya faru.
Ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta hanzarta lalubo bakin zaren
Inda ya ce ya na bayar da sako ne ga fadar shugaban tarayyar Nijeriya da ta dauki matakan yin maganin matsalolin tsaron da suke neman addabar kasar tarayyar Nijeriya.
“Hakika ba mu zabe su ba domin al’amura su kasance a cikin halin da suke ciki, a yanzu satar mutane ana neman kudin fansa,in mutum na tafiya hankali ba a kwance ba, a wurin aiki hankali ba kwance ba duk abubuwan da jama’a suke yi ba natsuwa saboda matsalar tsaro.
Manoma na kokarin ciyar da kasa da abinci amma sun shiga cikin halin tsaro don haka muke kira ga Gwamnati lallai su hanzarta sauke nauyin da ke kansu
Da yake tofa albarkacin bakinsa Fasto Yahana YD Buru kara yin kira ya yi ga daukacin al’ummar musulmi da Kirista da su hada kansu su tabbata an samu nasarar ciyar da kasa gaba.
“Muna godiya ga baban mu Shaikh Dahiru Usman Bauchi  bisa irin wanann damar da yake ba mu tsawon shekaru kusan Goma kenan ana wannan ziyarar duk lokacin da watan Azumi ya kama shi mun zo gidan nan an karfafa zumunci a tsakanin Juna hakika lamarin na bayar da ma’ana kuma ana samun ci gaba kwarai muna godiya kwarai Allah ya albarkaci zuri’a.
Taron bude bakin dai ya yi kyau tare da armashi kamar yadda aka saba gani a kowace shekara.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.