Home / Labarai / Marigayi Balarabe Musa Mutum Ne Mai Gaskiya Da Aiki Tukuru Domin Ci Gaban Kasa

Marigayi Balarabe Musa Mutum Ne Mai Gaskiya Da Aiki Tukuru Domin Ci Gaban Kasa

Imrana Abdullahi

 

An Bayyana tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, a matsayin mutum mai Gaskiya, Juriya da rikon Amana.

 

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada ya bayyana hakan lokacin da yazo gaisuwar rasuwar marigayin a gidansa da ke layin Aliyu Turaki a cikin garin Kaduna.

 

Lawal Sama’ila Yakawada ya bayyana cewa shi marigayin bai dauki rayuwa a bakin komai ba mutum ne mai saukin kai ganin girman kowa a koda yaushe kuma komai kankantar mutum marigayi zai ba mutum girman da Allah ya bashi a koda yaushe.

 

“Mutuwarsa ta nuna rayuwarsa ta nuna al’ummar da ya gina duk suna nan kuma duk dan siyasa ko mai mulki dole ya yi ko yi da wannan bawan Allah in an ki kuwa zai ga yadda za ta kasance mashi.

 

Ya kara da cewa “Hakika baba Balarabe abin ko yi ne ga mai son gaskiya kuma abin ki ne ga mara gaskiya, don haka babban rashi ne ga kasa baki daya.

 

Hakika babban rashi ne ga kasa baki daya ba Jihar Kaduna ko mutanen garin kaya ba kawai.

 

A gaskiya duk gudunmawar da zai bayar al’umma su ci gaba ne ya bayar don haka shi tashi ta yi kyau kuma Allah ne ya san wanda ya fi a cikin al’umma.

 

“Mutum ne mai daukar dimbin kalubale don kawai jama’a su ci gaba ya rika daukar irin wadannan kalubalan.

 

Kuma muna yin kira ga yan siyasa da su yi ko yi da wannan bawan Allah, in sun karkace hakika akwai sakamako kuma lokaci dai gasgata hakan domin a bayya ne lamarin yake, duk wanda yaki ji ba zai ki gani ba.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.