Home / Lafiya / Masari Ya Gargadi Ma’aikata Da Kada Su Karkatar Da Magunguna

Masari Ya Gargadi Ma’aikata Da Kada Su Karkatar Da Magunguna

Gwamna Aminu Bello Masari ya gargadi Ma’aikatan asibitoci da kada suyi gangancin karkatar da magungunan da Gwamnati ta samar domin amfanin al’ummomin karkara.
Gwamnan ya yi wannan gargadi ne yau a garin Kaita yayin da ya kaddamar da rabon magunguna ga asibitocin da ke cikin kananan hukumomi Talatin da hudu na Jihar baki daya.
Ya kara da cewa Gwamnati ta samar da wadannan magunguna ne domin saukaka wa al’umma musamman na karkara da kuma bunkasa kiwon lafiyar al’ummar jiha.
Gwamna Masari na katsina tare da sakataren Gwamnatin Jihar
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari suna tattaunawa da sakataren Gwamnatinsa Dakta Mustapha M Inuwa
Gwamna Masari ya kara da cewa Gwamnati ba za tayi sassaucin hukunci ba ga duk wanda aka kama da laifin yin almundahana a harkar sarrafa wadannan magunguna.
Kafin Gwamna Aminu Bello Masari ya tafi garin na Kaita, sai da ya halarci bikin tunawa da ranar Sojoji ta kasa wanda ake gabatarwa a kowace shekara a ranar Goma sha biyar ga watan Janairu.
Wadanda suka rufa wa Gwamnan baya a wajen wadannan bukukuwa sun da Mataimakin Gwamnan Alhaji Mannir Yakubu, Shugaban Majalisar Dokoki ta jiha Alhaji Tasi’u Maigari Zango, Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa, Wakilan Majalisar Dokoki ta jiha da na Majalisar zartaswa. da kuma Daraktocin Mulkin kananan hukumomi.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.