Home / Labarai / Mazauna Kasar Saudiyya Ne Kawai Za Su Yi Aikin Hajji

Mazauna Kasar Saudiyya Ne Kawai Za Su Yi Aikin Hajji

Mahukuntan kasar Saudiyya sun bayyana cewa yannkasar ne kawai za su yi aikin Hajjin Bana tare da yan asalin wadansu kasashen waje da suke zaune a cikin kasar ne za a bari su aiwatar da aikin hajjin na Bana.

 

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar aikin Hajji kasar ta fitar ta ce sun dauki mataki ne bisa la’akari da yadda cutar korona ta yadu zuwa kasahe sama da 180 a fadin duniya, da kuma adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar da wadanda ke dauke da ita da suka kai miliyan bakwai a fadin duniya.

Ga rashin riga-kafin annobar da ake fama da ita a duniya da kuma bukatar tabbatar da tazara tsakanin mutane da hana taron jama’a duka wadannan na daga cikin dalilan da ya sa aka soke Umara a bana, in ji sanarwar.

 

Sanarwa ta kara da cewa yadda cutar ke ci gaba da yaduwa da kuma yadda aka gaza samar da wata mafita in ba tabbatar da tazara tsakanin mutane ba, ya sa kasar za ta amince a yi aikin hajjin bana amma da ka’ida.

Ta ce aikin hajjin shekarar 1441 H/ 2020 D/ zai dauki mutanen da suke zaune a kasar ne kawai wadanda dama na zaune a saudiyya.

Saudiyya ta ce za a yi aikin hajjin tare da bin duk wasu hanyoyin da aka zayyana na kare mutane daga kamuwa da wannan annoba.

 

Za a bayar da tazara yayin aikin Hajjin kuma za a gudanar da shi kan doron koyarwar addinin musulunci kamar yadda aka saba.

Saudiyya ta dauki wannan matakin ne domin tabbatar da aminci ga duk wani mahajjaci da ke kasarta har sai sun koma kasashensu na ainihi

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.