Home / News / Mun So Buhari Yaje Majalisa Domin Amsa Dukkan Tambayar Da Za Su Yi Masa – Jama’a  

Mun So Buhari Yaje Majalisa Domin Amsa Dukkan Tambayar Da Za Su Yi Masa – Jama’a  

Mun So Buhari Yaje Majalisa Domin Amsa Dukkan Tambayar Da Za Su Yi Masa – Jama’a

 Imrana Abdullahi
Sakamakon irin yadda matsalar tsaro a tarayyar Nijeriya ke neman zamowa karfen kafa yasa tun bayan da aka yi wa wadansu masu aikin yankan Shinkafa a Jihar Borno da ke arewa maso Gabashin kasar, nan da nan yan majalisa wakilan al’umma suka yi ta Maza bayan kwashe tsawon lokaci ana takaddama tsakanin bangarori biyu da ke majalisar sai suka yanke hukuncin kiran shugaba M8hammadu Buhari ya gurfana a gabansu domin amsa tambayoyin da za su masa.
Sakamakon irin yadda wasu Gwamnonin APC suka mayar da lamarin ya zama siyasa duk da irin yadda ake kashe jama’a a garuwa da kauyukan Jihohin da suke cewa suna yi wa shugabanci.
Kamar yadda wakilinmu ya ji ta bakin jama’a wasu sun bayyana lamarin tsaro a Nijeriya da cewa shi ne ya haifar da matsanancin talaucin da jama’a suke ciki, kasancewa daman kudi sai daga wurin Gwamnati kawai suke fitowa amma ga shi matsalar rashin tsaro a halin yanzu ta lashe dukkan dukiyar jama’a da ya dace su mutane masu ita su yi amfani da ita.
“Ana kwashe Dukiya ne kawai ana mikawa wasu yan tsirarun mutane da sunan kula da harkar tsaro amma har yanzu babu tsaron sai kashe jama’a kawai ake yi ba ji ba gani, ana kwashe dukiyar mutane, an hana manoma kwashe amfanin Gonakinsu sai sun biya yan bindiga, masu satar jama’a kudin da suka nemi su ba su lamarin dai kamar ba Gwamnati a kasar”.
Wasu mutane da wakilinmu ya zanta da su sun shaida masa cewa a matsayinsu na wadanda suka zabi Muhammadu Buhari da kuri’unsu kuma suka yi aiki da dukiyarsu tun da Buhari ba kudi yake bayarwa ba koda yana da kudin, sun yi tsammani Buhari zai je majalisa ya tsaya gaban yan majalisa ya amsa dukkan tambayar da za su yi masa amma sai ga wasu yan tsirarun mutane wadansu ma sun ci albarkacin irin goyon baya da soyayyar da Talakawan Nijeriya suke yi wa Buhari ne sannan suka zama Gwamnoni, da yawa daga cikinsu ko zaben karamar hukuma ba za su iya ci ba amma Talakawa suka mayar da su Gwamnoni dalilin Buhari sai gashi sun ba talakawan kunya sun tilastawa Buhari kada yaje majalisa ya amsa tambaya”.
Wasu kuma sun shaidawa wakilinmu cewa mun yi tsammanin Buhari ba zai taba gujewa wani ko wasu da ke son yi masa tambaya a kan harkokin da suke gudana a karkashin Mulkinsa don haka ya daina gayawa yan Nijeriya laifin wane ko su wane ne suka bata kasa a can baya shi a yanzu ta tabbata ya kasa gyarawa kuma ” mun zabe shi ne domin a samu gyara da tunanin zai iya don haka a yanzu sai mu ci gaba da yi wa Allah Istigifari domin ya fitar da mu ya bamu wani shugaban da zai iya amma Buhari ya yi mana bazata”.
Wasu kuma suka ce kafin Buhari ya dare karagar mulkin Nijeriya mun yi tsammani jajirtaccen shugaba ne muka zaba sai ga shi irin abin da yake fadi da bakinsa har Talakawa suka amince da shi lamarin ba haka yake ba a aikace, jama’a birni da kauyuka na zaune a cikin rashin natsuwa, mun duba a majalisa muga isawar Buhari amma sai shuru kuma ya kasa gaya mana dalilin rashin zuwansa majalisar.
Wasu kuma sun ba Buharin ne shawara da cewa ya daina amincewa da shawarar irin wadannan rukunin mutane da sunan Gwamnonin APC domin za su lalata masa mutuncinsa a wurin jama’ar da suka zabe shi wato Talakawa, kamata ya yi Buhari ya tattara Talakawa yaji me suke Bukata amma ba cima zaune ba da suke yin abin da suka ga dama da dukiyar talakawan kasa.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.