Home / Labarai / Muna Shawartar Masu Yawan Shekaru Su Zauna A Gida – El- Rufa’i

Muna Shawartar Masu Yawan Shekaru Su Zauna A Gida – El- Rufa’i

 Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I, ya shawarci masu yawan shekaru da su zauna a gida domin tsira da lafiyarsu a lokacin cutar Korona Bairus.
Gwamna Malam Nasiru Ahmad El – Rufa’i ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake yi wa al’ummar Jihar jawabi game da cire dokar zaman gida
“A lokacin da muka bude, muna shawartar masu yawan shekaru da ke cikin al’umma da su zauna a gida domin tattalin lafiyarsu saboda yinnhakan zai taimaka wajen rage batun zuwa gaisuwa da kuma halartar Jana’iza. Mutanen da suke da shekaru 50 lallai su kiyayi karbar masu zuwa masu ziyara”.
“Idan kuma har ya zama dole sai an karbi baki to ya dace a tsaya nesa nesa a kalla motoci biyu tsakaninka da wanda ya ziyarci ka. Masu kananan shekarun da za su iya kamuwa da cutar Korona amma kuma ba za su nuna alamun hakan ba, za su iya sanyawa masu yawan shekaru cikin sauki”.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa Gwamnatinsa ” za ta ci gaba da kwashe Almajirai ana mayar da su zuwa ga uyayensu domin iyayen su kula da su saboda suna da yancin a ilmantar da su”. Inji Gwamnan kaduna.
Kamar yadda ya ce ” wannan wani mataki ne na kokarin bin dokar inganta rayuwar yara, yaro zai iya samun ilimin boko da na addini ba tare da an yi watsi da shi ba wanda hakan ke yin jagoranci wajen a rika cin mutuncin yara har su kasa samun makoma mai kyau a cikin rayuwarsa.
El Rufai ya bukaci al’ummar Jihar Kaduna da su tabbatar da aiwatar da abin da ya rataya a wuyansa.
” Bari mu tabbatar da ganin irin yadda muka sadaukar a lokacin dokar hana fita ya zaman mana mabudin ci gaba da taimakawa kawunanmu ba tare da yin wautar barin cutar ta ci gaba da yaduwa ba da har za ta kai ga mutuwar jama’a da dama.
Jama’a sun sadaukar tsawon sati Goma a lokacin dokar zaman gida. Don haka ya dace mu nuna cewa zamu iya zama lafiya a lokacin sassauta dokar ta hanyar bin dokokin da aka Sanya sau da kafa”.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.