Home / Lafiya / Mutane 305 Ne Ke Dauke Da Cutar Korona A Nijeriya

Mutane 305 Ne Ke Dauke Da Cutar Korona A Nijeriya

Daga Abdullahi Daule da rahoton
A sababbin alkalumman da hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta fitar sun bayyana cewa a halin yanzu akwai mutane 305 da suke dauke da cutar a tarayyar Nijeriya baki daya.
Hukumar ta bayyana cewa faruwar hakan ya biyo bayan irin yadda aka samu mutane Goma sha Bakwai (17) ne da suka kamu da cutar a jihohi daban daban da suka hada da Kaduna, katsina, Abuja da sauransu.
Hukumar dai na kara yin kira ga daukacin jama’a da su ci gaba da kiyaye wa da matakan hana yaduwar cutar a tsakanin jama’a da suka hada da wanke hannu a kai a kai a kalla duk bayan Mintuna 30 kiyaye wa da masu yin atishawa, tari da kuma yawan taba idanu ko hanci da hannigan mutum da kuma diana shiga ko zama a cikin cinkoson jama’a.
A cikin wannan adadin mutane 17 da aka samu sun kamu akwai daya a kaduna da 3 saga Jihar katsina da suka kasance Iyalan Likitan da ya mutu ne a garin Daura sakamakon cutar inda matarsa da yayansa biyu duk aka same su sun kamu da cutar Covid – 19 da ake cewa Korona bairus.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.