Home / News / SANATA UBA SANI Ya Tallafawa Marayu A Bikin Murnar Cikarsa Shekaru 50

SANATA UBA SANI Ya Tallafawa Marayu A Bikin Murnar Cikarsa Shekaru 50

SANATA UBA SANI Ya Tallafawa Marayu A Bikin MurnarbCikarsa Shekaru 50
Mustapha Imrana Abdullahi
Domin tabbatar da kiyaye doka da ka’idar yaki da cutar Korona, Sanata Uba Sani mai wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya a satin da ya gabata ya takaita batun taron murnar cikarsa shekaru 50 inda ya mayar da bikin ya zama Sanya murna da farin ciki a fuskokin marayu dari 800 a gidaje hudu a fadin mazabarsa.
Tallafin domin marayu su samu sauki, an bayar da shi ne ta hannun mai kula da gidauniyar Sanata Uba Sani, kuma mutane sama da  dari 800 ne suka ci gajiyar tallafin da ke a gidan marayu hudu da suka hada da Ummu Atyam gidan marayu da ke Unguwar Dosa, sai gidan marayu na Addonai a Barnawa, gidan marayu na Naphatali a Gonin Gora da kuma gidan marayu na Al- Ihsan, da ke Unguwar Nasarawa.
Wannan kokarin da Sanata Uba Sani ya yi wata hanya ce ta nuna tausayi da jin kan jama’a musamman marayu da suke bukatar a taimaka masu, hakan ta sa Sanata Uba Sani ya shirya bikin murnar ranar haihuwarsa domin taimakon mabukata da yake tabbatar da irin yadda a matsayinsa na dan majalisa mai wakiltar dimbin al’ummar birni da karkara zai nunawa jama’a muhimmancin da suke da shi a wurinsa, kuma hakan zai sa irin wadannan mutane su san cewa ba a mance da su ba.
Sanatan ya zabi ya gudanar da bikin ranar haihuwarsa ta irin wannan hanyar duba da yadda kasar nan take ciki inda ake bukatar kiyaye doka da ka’idojin yaki da cutar Korona da ta addabi duniya.
 Da yake jawabi a wajen taron wakilin Sanata Uba Sani ya yi bayanin cewa a irin wannan yanayin kalubalen mawuyacin lokaci Sanya annuri, farin ciki da annashiwa ga fuskokin irin wadannan mutane marasa karfi da galihu a cikin al’umma yana da matukar amfani kwarai.
“Babu ta yadda zamu rika cewa muna so da Kaunar Allah, amma kuma mu kasa kula da irin halin kuncin da wasu mabukata ke ciki a tsakanin al’umma”, ya kara jaddada.
Kayan da aka Tallafawa marayun da su sun hada da Barguna, kayan amfani a dakunan zagayawa da dai sauransu duk gidajen marayun sun samu amfana da kayan.
Dukkan mutanen gidajen sun yi addu’o’I ga Sanata Uba Sani na fatan alkairi da kuma nema masa taimakon Allah a dukkan baki dayan rayuwarsa ta duniya da kiyama.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.