Home / Labarai / Talban Danejin Katsina Kalubale Ne A Gare Ni – Labiru Musa Kafur

Talban Danejin Katsina Kalubale Ne A Gare Ni – Labiru Musa Kafur

Talban Danejin Katsina Kalubale Ne A Gare Ni – Labiru Musa Kafur
Mustapha Imrana Abdullahi
Talban Danejin Katsina Alhaji Labiru Musa Kafur ya bayyana cewa ana ba mutane Sarauta ne sakamakon irin kokari da jajircewa da suke yi wajen ci gaban al’umma.
Duk da yake ba kasafai ake samun  mutum ke wasa kansa da kansa ba amma dai ina ganin dalilin da ya sa aka ba ni wannan sarautar ta Talban Danejin Katsina an yi la’akari ne da irin kokarin da nake yi  domin samawa jama’a ci gaban da ya dace ta yadda rayuwarsu za ta inganta.
Alhaji Labiru Musa Kafur ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilinmu.
” Bayan na yi aikin koyarwa kuma na yi shugaban sakandare a Dankanjiba, na dai yi aikin shekaru 35 wanda ya hada da aikin babban Sakatare na tsawon shekaru Ashirin (20) don haka shi Danejin Katsina wanda yakasance mutum ne mai ilimin addini sosai da ke tafiya da zamani ya yi la’akari ne da irin gudunmawar da muke bayarwa hakan ya sa aka ba ni Sarautar Talban Danejin Katsina.
Labiru Kafur ya ci gaba da cewa ” akwai lokacin da suka yi aiki a kwamitin aikin Hajji tare da Danejin Katsina wanda mun samu ci gaba da dama hakan ta Sanya har wasu daga wadansu wuraren sai da muka taimaka masu, hakan ta Sanya an samu kyakkyawar fahimta da ingantacciyar nasara.
Ya kara da cewa hakan ta Sanya duk wadansu abubuwa nasa ya na tuntuba ta kwarai domin jin shawara da abin da ya dace ta hanyar bayar da shawara tsakani da Allah,wannan dangantaka ta yi tasiri kwarai.
“Batun zaman lafiya da kokarin ciyar da al’umma gaba musamman matasa, gudunmawa shawarar da za ta ciyar da Gundumar gaba domin kara inganta al’amura.
Wannan nadin na matsayin yan majalisar Danejin Katsina ne Hakimin Mahuta da za a ci gaba da aiwatar da ayyukan ciyar da al’umma gaba, domin idan mutum bai bayar da gudunmawa ga jama’arsa ba to, a ina zai bayar? ai inda ka fito nan ne gaba kafin ka tsallaka wani wuri, wadannan dalilai ne kadan daga cikin abin da ya sa aka nada ni Talban Danejin Katsina.
Za mu ci gaba da yin nuni a game da dukkan al’amura baki daya, muna kuma rokon Allah ya ci gaba da tabbatar mana da nasara ya ciyar da Gundumar Mahuta,Karamar hukumar Kafur, Jihar Katsina da Nijeriya baki daya gaba”.

About andiya

Check Also

Emir, Beneficiaries Says Dangote Food Intervention Impactful In Nasarawa, Adamawa, Others

The Aliko Dangote Foundation (ADF) has received a torrent of accolades as it continued to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.