Home / KUNGIYOYI / Wasu Mutane Na Kokarin Yi Wa Kungiyar Dillalai  Zagon Kasa – Shafi’u Kwamanda

Wasu Mutane Na Kokarin Yi Wa Kungiyar Dillalai  Zagon Kasa – Shafi’u Kwamanda

Wasu Mutane Na Kokarin Yi Wa Kungiyar Dillalai  Zagon Kasa – Shafi’u Kwamanda
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban hadaddiyar kungiyar Dillalan Gidaje, Filaye na Jihar Kaduna Shafi’u Salisu Abubakar da ake yi wa lakabi da Shafi’u Kwamanda, ya fito fili ya bayyana cewa bisa irin sahihan bayanan da suka samu a halin yanzu wadansu mutane na kokarin ganin sun yi wa kungiyar da suka kafa zagin kasa.
Shafi’u Salisu ya bayyana hakan ne a wurin wani babban taron da suka yi na yayan kungiyar wanda shugabannin yankin shiyyar Kaduna ta tsakiya suka shirya da aka yi a dakin taro na gidan tunawa da Sardauna a Kaduna.
Shafi’u wanda shi ne shugaban kungiyar Dillalan Gidaje da Filaye na Jihar Kaduna ya ce sun kafa wannan kungiya ne domin kara karfafa tsaro da ci gaban kungiyar tare da yayanta baki daya.
Wasu mata yayan kungiyar kenan da suka halarci taron shiyyar na Kaduna.
“Kasancewarmu masu sana’ar da ta fi kowace sana’a martaba da daraja a cikin al’umma muka ga ya zama wajibi a daina zaman kara zuba wannan yasa muka hada kanmu domin samar da kungiyar da kowane Dillali zai dogara da ita domin ta yi jagoranci wajen share mana hawaye”.
Shafi’u Salisu ya ci gaba da cew ” Mun samar da Fom tare da yi wa kowane dan kungiya katin shaidar zama dan kungiya, wanda dole sai da katin shaidar dan kungiya ne mutum zai iya sana’ar saye ko sayar da filaye ko gidaje ko kuma yin harkar karbar wa wasu kudi saboda muna bukatar a samar da tsafta”.
Ya kuma tabbatar da cewa wadansu mutane daga wasu Jihohin kasar nan tun daga yankin Arewa zuwa yankin Kudancin Nijeriya tuni duk sun yi koyi da irin tsarin da Jihar Kaduna ta dauka na samar da kungiyar Dillalan Gidaje da Filaye a Jihar su.
Yayan kungiyar daga ko ina cikin Jihar kaduna suka halarci taron, an kuma tattauna batutuwa da dama da za su kara inganta sana’ar Dillanci.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.