Home / Labarai / Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 1,Sun Sace Mata 2, Maza Uku Sun Harbi Biyu A Maska Jihar Katsina

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 1,Sun Sace Mata 2, Maza Uku Sun Harbi Biyu A Maska Jihar Katsina

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 1,Sun Sace Mata 2, Maza uku Sun Harbi Biyu A Maska Jihar Katsina
Mustapha Imrana Abdullahi
Al’ummar garin Maska da ke karamar hukumar Funtuwa Jihar Katsina sun koka matuka sakamakon rashin tsaron da yake addabarsu lamarin da ya haifar masu da asarar rai da lafiyar mutanen garin da kewaye.
Ga duk wanda ya san tarihin garin Maska ya san cewa wuri ne mai cikakken tarihi musamman ganin cewa tarihin masarautar Katsina ba zai cika ba sai an hada da Maska.
Wannan babban gari da jama’ar cikinsa ke kokarin taimakawa wajen ci gaban tattalin arzikin Nijeriya musamman ta fuskar Noma da kuma aikin Gwamnati kasancewar garin na da dimbin ma’aikata masu aiki a matakan kananan hukumomi, Jiha da tarayya baki daya, amma sai ga shi a yanzu zaman wannan babban gari mai tarihi na nema ya gagara saboda irin yadda yan Ta’adda ke cin karensu ba babbaka a duk lokacin da suka shigo cikin garin na Maska.
Hakan ta sa wakilinmu ya tuntubi wani dan asalin garin kuma mazaunin garin Alhaji Rabe Mela Maska, game da abin da ya faru a jiya cikin dare.
Alhaji Rabe Mela Maska ya shaidawa wakilinmu cewa wasu yan Ta’adda ne suka zo garin nasu cikin daren Jiya Juma’a inda suka kashe mutum daya mai suna Alhaji Salmanu, ta hanyar harbi da bindiga.
Sai kuma wasu mutane biyu da suka hada da Ya’u da Ibrahim da suka harba daya a kafa dayan kuma a hannu suna asibiti ana duba lafiyarsu, sai kuma kwanan baya kamar yadda majiyarmu ta bayyana mana a kwanan baya ma sun kashe wani mutumin garin Gangara kan iyakar Jihar Kaduna da Katsina, duk kusa a marabar Maska a karamar hukumar Funtuwa Jihar Katsina.
Rabe Mela Maska ya ci gaba da cewa zuwan yan bindigan sau uku kenan garin Maska, inda suka dauke mata biyu tun a can baya saboda kasancewar garin na Maska babu wani tsaro ko kadan, ko ofishin yan Sanda ma babu.
Don haka suke yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya hanzarta bayar da umarni ga shugaban yan  sandan Nijeriya da a samar da tsaro ta hanyar samar da ofishin Yan Sanda domin tabbatar da tsaron dukiyar jama’a a wannan yankin.
“Mu ya dace a Sani cewa tsohon gari mai tarihi kamar Maska amma an mayar da shi Juji ba tsaro ba komai ga shi a yanzu masifar da ta fada wa garin na zuwan yan Ta’adda a duk lokacin da suka ga dama, wurin na neman lalacewa baki daya.
“An dauki mutane uku a daren jiya da suka zo ta’addanci a garin Maska kuma a halin yanzu ba a san halin da suke ciki ba”.
Mela ya kara da cewa “Akwai wadansu matan da aka dauke su biyu da goyonsu,matan wani mutum mai suna Bilya, kowace ta na da goyon kananan yara a goye  kanana kwarai da aka dauke su tare da mijinsu, amma kasancewar mijin mai jiki ne ba zai iya tafiya ba  sai suka sake shi bayan sun yi masa dukan tsiya  sannan suka jafar da shi suka ta fi da matan dajin da ba a san halin da suke ciki ba a halin yanzu, a kalla sun yi sati uku a hannun yan ta’addan”. Inji Mela.
A daren jiya an sace mutane uku duk Maza an kuma ta fi da su daji wanda a halin yanzu babu wanda ya san halin da suke ciki sai Allah.
A bisa wadannan dalilai ne mutanen yankin Maska da kewaye suke yin kira ga Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da kuma shugaban Yan Sandan Nijeriya da cewa a sama masu da katafaren ofishin Yan Sanda a yankin Maska baki daya saboda a halin yanzu haka nan suke babu komai ba tsaro wanda hakan yasa yan bindiga suke aiwatar da ta’addancinsu yadda suke bukata kuma a lokacin da suka so.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.