Home / Labarai / Yar Shekaru 34 Ta Haifi Yaya 17 A Zariya

Yar Shekaru 34 Ta Haifi Yaya 17 A Zariya

 Imrana Abdullahi
Wata mai shekaru 34 ta haifi yaya 17 a haihuwar da ta yi sau , wadda ta haifi yaya hudu a halin yanzu
Kamar yadda wakilinmu ya samu cikakken bayani daga birnin Zariya cewa matar mai shekaru 34 mai suna Hauwa’u Sulaiman, wadda takasance matar aure ce ta samu cikakkiyar nasarar haihuwar yaya hudu a Zaroya.
Matar auren, Hauwa’u Sulaiman, da ke zaune a gida mai lamba 70 unguwar Alfadarai a birnin Zariya Zariya samu nasarar haihuwar yaya hudu a ranar Juma’a 5 ha watan Yuni, 2020, a asibitin Gambo Sawaba, da ke Kofar Gayan, Zariya, amma an mayar da ita asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ita da jariran da ta Haifa domin samun kulawa ta musamman.
A lokacin da Malama hauwa’u Sulaiman ke zantawa da wakilinmu ta shaida masa cewa kafin a kawo su asibitin ABUTH da ke shika, Namijin cikinsu ne kawai ya rasu, yanzu saura mata uku da a yanzu haka suke samun kulawa ta musamman, ita kuma tana samun kulawa a wurin da ake kulawa da wadanda suka haihu na asibitin.
Hauwa’u, ta ci gaba da cewa duk da cewa tana cikin koshin lafiya, amma saboda shawarar Likitoci sai aka ce ya dace ta samu kulawa sosai, kuma a kan haka a yanzu an kara mata jini leda biyu.
Kamar yadda ta ce a yanzu haihuwarta ta 8 kenan inda ta samu yaya 17 kuma duk a wadannan haihuwar da ta yi a yanzu ne kawai likitocin sula ce mata tana da hawan jini.
Da yake jawabi mijin hauwa’u, Malam Sulaiman, wanda ya kasance yana sana’ar tukin mota ne ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa wannan kyautar da ya yi masa kuma sun taba samun yaya uku har sau biyu yaya biyu kuma sau biyu haihuwar yaya daya kuma sau uku shima kuma a yanzu sai ga yaya hudu baki daya Allah ya ba su.
Ya ci gaba da cewa ko a wadancan yayan uku da suka Haifa ma dan Uwansa ne ke tallafawa a duk lokacin da bukata ta taso.
Mahaifiyar Hauwa’u, mai suna Saudatu Haruna, cewa ta yi lamarin haihuwar Hauwa’u gado ne tun daga kakanni da kuma ita kanta saboda ko ita ma ta haifi yan biyu sau uku.
Ta bayar da bayanin irin yadda mahaifiyarta ta haifi yan uku, kuma mahaifinta shima yan tagwaye ne, ta kara da cewa don haka irin haihuwar da Hauwa’u take yi bai zo da mamaki ba sai dai kawai a duk cikin yan uwanta ita kadai ce take taba haihuwar yaya hudu a lokaci daya
A lokacin da tawagar manema labarai da suka ziyarci asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya inda aka kai su domin Uwar da yayanta su samu cikakkiyar kulawar kiwon lafiya, babban Likita mai ayyukan bayar da shawara, Dokta Isa Abdulkadir cewa ya yi dukkan Marian guda uku suna cikin koshin lafiya kuma a halin yanzu suna samun kulawa daga tawagar kwararrun Likitoci.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.