Home / News / Za A Gina Katafaren Asibitin Gwamnatin Tarayya A Rigasa- Uba Sani
Hoton
Ga hoton sanata Uba Sani

Za A Gina Katafaren Asibitin Gwamnatin Tarayya A Rigasa- Uba Sani

Mustapha Imrana Abdullahi
Sanata mai wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa akwai kyakkyawan tsarin da za a gina katafaren asibitin Gwamnatin tarayya a unguwar Rigasa.
Sanata Uba Sani Sani shi ne shugaban kwamitin harkokin Bankuna da kudi tare da al’amuran harkokin bashin kasashen waje na majalisar Dattawa ya fayyace batutuwa da dama a tattaunawar.
Sanata Uba Sani ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da kafafen yada labarai a Kaduna.
Uba Sani ya ci gaba da cewa tuni ya kai wannan batu a majalisar Dattawa kuma batun samar da asibitin Gwamnatin tarayyar ya samu karbuwa.
“Idan an gina wannan asibitin zai yi daidai da na ko’ina a kasa da duniya baki daya saboda za a samar wa asibitin ingantattun na’urorin da duk wani asibiti ya dace ya samu”.
Idan kuma an samar da asibitin zai taimakawa dimbin jama’a daga wurare daban daban daga ciki da wajen Nijeriya saboda kwararrun Likitoci malaman asibiti da kuma kayan aiki.
Sanata Uba Sani ya kara da cewa tuni aka yi wa kudirin samar da kwalejin ilimi a karamar hukumar Giwa.
“Akwai tsari na nan na samar da hukumar kula da Gandun Daji da bincike a yankin karamar hukumar Birnin Gwari domin kara inganta al’amuran bincike da yawon shakatawa kasancewar birnin Gwari wuri ne mai katafaren Gandun Dajin da za a iya yin amfani da shi ta fuskar ci gaba.
‘Na so ne in canza alkiblar siyasar arewa baki daya saboda ina da wani shirin yi wa mutane ingantaccen tsarin horo na akalla mutane 1000 da yardar Allah”.
Ya kuma yi kira ga yan siyasa da cewa daga zarar an kammala zabe a ajiye bambancin siyasa ta yadda al’umma za su amfana da tsare tsaren Gwamnati da mutanen arewa basa amfana da su duk da ya dace kowa ya amfana amma saboda rashin kishin zababbun yan siyasa da yaudara mutane  arewa basa amfana da tsarin gwamnatin na tarayya.
Ya kuma tabbatar da cewa batun samun bashin da Jihar Kaduna ke nema lamarin tuni ya nuna, illa dai akwai wadansu bangarori da hukumomin Gwamnati tare da ma’aikatun da suke bukatar bashin.
“In an dade watan Maris Gwamnati  Jihar Kaduna za ta samu bashin da take bukata, wanda idan an samu kudin dala miliyan sama da dari uku za a samu bunkasar harkokin ilimi,lafiya, Tattalin arziki da bunkasar Jihar kaduna baki daya.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.