Home / Kasuwanci / Za A Kara Bude Bankin Mortgage A Zariya Da Kano – Dankane

Za A Kara Bude Bankin Mortgage A Zariya Da Kano – Dankane

Daga Imrana Abdullahi Kaduna

Wani daga cikin shugabannin Bankin gina gidaje na tarayyar Nijeriya Alhaji Umar Dankane Abdullahi, ya bayyana aniyar da suke da ita na bude karin ofishin Bankin a garuruwan Kano da Zariya cikin Jihar Kaduna domin jama’a su ci gaba da cin gajiyar ayyukan Bankin.
Alhaji Umar Dankane ya bayyana hakan ne a garin kaduna lokacin da ya halarci bikin ranar Bankin a kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke Kaduna.
Manyan jami’an Bankin Morgage lokacin da suka halarci kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna
Alhaji Dankane wanda ya wakilci shugaban Bankin Alhaji Ahmed Musa Dangiwa ya ce sun yanke shawarar kara wadannan Ofisoshi biyu ne saboda irin bukatar da ake da ita domin ma’aikata da sauran Jama’a su ci gaba da cin gajiyar tsare tsaren Bankin cikin sauki.
Ya kara da cewa suna ba ma’aikata bashin gyaran gidaje da kuma samar masu da gidaje a gine kuma har da kungiyoyin Gama kai ma suna cin gajiyar Bankin domin akwai shirin da aka yi wa kowa kasancewar ana bukatar kowane dan kasa ya rika yin ajiya a Bankin indai yana samun kudin da suka kai naira dubu uku duk tanajen tanajen na nan a tsare domin Jama’a.
A dama shugaban shiyya na Bankin Morgage tare da shugaban kungiyar manyan ma’aikata TUC Kwamares Shehu Muhammad a wajen taron Bankin a kaduna
Sai dai ya yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta kara yawan jarin Bankin kasancewar jama’ar Nijeriya sun yi yawa a halin yanzu kuma akwai bukatar samun gidaje da yawa a yanzu.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban kungiyar manyan ma’aikata (TUC)na Jihar Kaduna Kwamared Shehu Muhammad cewa ya yi hakika ma’aikata a Jihar kaduna sun ci gajiyar wannan Banki domin wasu tuni aka ba su kudin gyaran gidajensu a wannan Banki.
(Don haka ya dace Gwamnati ta zuba manyan kudi a Bankin domin kara fadada cin gajiyarsa).

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.