Home / Lafiya / Za A Lashe Cutar Lassa Baki Daya Daga Nijeriya – Ministan Muhalli

Za A Lashe Cutar Lassa Baki Daya Daga Nijeriya – Ministan Muhalli

Mustapha Imrana Abdullahi
Ministan ma’aikatar kula da muhalli na tarayyar Nijeriya Dakta Muhammad Mahmud Abubakar, ya bayyana cewa Gwamnati ta kammala shiri tsaf domin lashe cutar Lassa da Bera ke haddasawa daga kasar baki daya.
Ministan ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron gangamin fadakar da jama’a kan illar cutar da kuma abin da ke haifar da ita tare da hanyoyin daukar matakan magance ta baki daya.
An dai gudanar da taron gangamin ne a unguwar Hayin Rigasa a filin makarantar Firamare ta Takwaja a Kaduna.
Ministan kula da muhallin ya tabbatar wa da daukacin al’ummar kasar cewa an shirya yi wa Bera dirar Kare dangi Baki daya domin kakkabe beraye a cikin al’umma, kasancewarsa mai haddasa cutar.
Minista Muhammad Mahmud ya ci gaba da bayyanawa taron gangamin jama’ar cewa kashi 80 cikin  dari na cututtuka na samuwa ne sakamakon gurbataccen muhalli
Saboda haka ne ma’aikatar za ta yi amfani da jami’an duba gari na ma’aikatar domin shiga lunguna da sako tare da shiga gidaje domin fadakar da jama’a illar bera da kuma abin da ya dace ayi.
“Fitsari, Kashi da dukkan jikin Bera na dauke da cutar Lassa don haka sai an kiyaye kada a kashe bera ko bera ya mutu a dauke shi da hannu domin a jefar,a dai yi amfani da wani abu don kada a taba bera baki daya”.
Ministan ya bayar da tarihin yadda cutar ta samo asali a wani gari a cikin Jihar Barno a gari mai suna Lassa don haka ne bisa yadda al’amuran harkokin lafiya ke tafiya idan an samu bullar cuta a wuri sai kawai a Sanya mata sunan wurin da aka same ta.
Minista Mahmud ya kuma shiga wani gida tare da tawagarsa inda ya Sanya maganin beraye a cikin wani daki da kuma wadansu wurare a cikin gidan domin fara aikin a aikace daga wurinsa matsayin nunin yadda za ayi aikin fadakarwar.
An kuma yi jawabai da dama a wajen taron domin bayyana yadda cutar take da kuma yadda za a dauki matakin magance faruwar hakan musamman ta hanyar yi wa beraye dirar mikiya da tsaftar muhalli a ciki da wajen gidaje tare da unguwanni baki daya.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.