Home / Big News / FARUK SULEIMAN ( FASMAN) NE SABON SHUGABAN KASUWAR DUNIYA TA KADUNA

FARUK SULEIMAN ( FASMAN) NE SABON SHUGABAN KASUWAR DUNIYA TA KADUNA

 

Daga Imrana Abdullahi
Bayan kammala Babban Taron shekara shekara da Ake yi na masu ruwa da tsaki da dukkan mambobin da suka yi rajistar Zama mambobin Kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna, Jim Kadan bayan kammala Taron sai aka Zabi sababbin shugabannin da za su ja ragamar tafiyar da kasuwar na tsawon shekaru biyu kamar yadda Yake a ka’idar.
Faruk Suleiman da Ake yi wa lakabi da FASMAN NE ya samu nasarar da Allah ya zabe Shi ya Zama shugaban Baki daya.
An dai Zabi mutane Takwas da za su yi aiki tare da Faruk Suleiman aatsayin shugabanni
Kuma an rantsar da su kamar yadda dokar kasa ta tanada, kamar yadda zaku iya gani a cikin hotunan nan.
Da Yake yi wa Manema labarai jawabin sabon shugaban Alhaji Faruk Suleiman cewa ya yi sabon zamani ya Fara inda ya yi alkawarin tabbatar da cewa zai yi dukkan abin da ya dace domin ganin an samu ci gaba Mai ma’ana.
Ya kuma yi alkawarin ciyar da harkar Noman musamman Kiwon Dabbobi da nufin Samar da ingantacviyar lafiya GA al’ummar kasa Baki daya.
Ina kuma yin Kira ga daukacin mambobin wannan babbar Kasuwar duniyar kasa da kasa da su BA mu cikakken Hadin Kai da goyon baya ta yadda za a samu nasarar da kowa ke bukatar.
Ya kuma bayyana wata garabasa GA dukkan masu Kamfanonin kansu da su samu Fom a nan take wajen Taron su cika su kuma biya kashi ashirin da biyar na kudin da ya dace su biya za su samu satifiket din su a cikin Dan kankanin lokaci

About andiya

Check Also

Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861 Ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.