Home / KUNGIYOYI / Masu Bukatar Musamman Sun Yi Murnar Samun Dokar Ƴanci A Kaduna, Sun  Buƙaci Aiwatar Da Dokar Nan Take

Masu Bukatar Musamman Sun Yi Murnar Samun Dokar Ƴanci A Kaduna, Sun  Buƙaci Aiwatar Da Dokar Nan Take

 

DAGA; USMAN NASIDI KADUNA.

 

 

HADADDIYAR kungiyar nakasassu ta kasa (JONAPWD), reshen jihar Kaduna ta nuna farin cikin ta game da samun Dokar ƴancin nakasassu da aka dade ana jira wadda aka sanya cikin doka kuma Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufai ya sanya wa hannu.

 

 

A yayin ganawa da manema labarai a Cibiyar Kungiyar Nakasassu ta Kaduna, Shugaban Suleiman Abdulazeez ya yi bayanin cewa JONAPWD reshen jihar Kaduna ne ta kirkiro da kudirin a karkashin jagorancin Kwamared Rilwan M, Abdullahi a shekarar 2009 wanda a lokacin yana matsayin wani kudiri mai zaman kansa.

 

 

Suleiman ya kara da cewa, manufar kudirin dokar da aka gabatar a lokacin ya kasance don ya zama na yau da kullun ne tare da shigar da nakasassu cikin harkokin al’umma.

 

 

Dokar ita ce za ta tabbatar da cewa nakasassu suna da hakkoki da dama iri ɗaya kamar kowa, haka kuma tana ba da dama daidai wa daida da nakasassu a cikin jama’a, har da fannin kamfanoni masu zaman kansu don samun damar gudanar da harkokinsu daidai gwargwado.

 

 

Ya ce, “a lokacin yakin neman zabe na shekarar 2015, Gwamnan Jihar Kaduna ya janyii mutane masu nakasa cikin tafiyarsa kuma tare da yi musu alkawari a kan idan aka zabe shi zai dauki kudirin a matsayin Dokar Zartarwa, kuma ta hanyar tsawaita wannan alkawari, Mai Girma ya cika alkawarinsa, hakazalika zai zama wata kwangilar zamantakewa tsakanin wannan gwamnatin yanzu da nakasassu a jihar Kaduna. ”

 

 

 

“Muna farin cikin sanar da wannan mahada cewa a ƙarshe an sanya dokar a matsayin doka, Mai Girma Gwamna ya cika alkawuran da ya yi wa nakasassu a jihar, wanda Inda ba don haka ba, toh da wannan dokar ba za ta samu nasara ba, amma daga karshe Gwamnan Jihar ya rattaba hannu a kan Dokar naƙasassu ta Jihar Kaduna bayan sama da shekaru 10 tare da gudunmuwar Kungiyoyi na ba da agaji,

 

Ƙungiyoyin Jama’a da Kafafen Yada Labarai wadanda suka tallafa don tabbatar da Dokar ta ga hasken rana. ”

 

 

“Hakanan tare da kokarin wasu masu ruwa da tsaki da suka dace kamar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Ma’aikatar Ayyuka da Ci Gaban Jama’a, Ma’aikatar Shari’a, Kwamitin Gyaran Jihar Kaduna, Accountability Lab, PERL, CALPED, SAVI, CCD, Sight Saver, Gender Working Group da Dakta Hajiya Amina Salihu tsohuwar shugabar hukumar gyaran fuska, Alhaji Musa Zubairu Kwamishinan dindindin na hukumar Majalisar, wanda da hakan ya dawowa da yaranmu burinsu.

 

 

“Mun yi imani da gaske cewa wannan nasarar da Babban Gwamnan Jihar Kaduna ya samu za ta fitar da membobinmu daga cikin jangin zama a kan titi, ta share gogewar nuna wariya da shinge da Al’ummar mu ke fuskanta don shiga cikin dukkan bangarorin Al’umma.” – Inji Shugaban.

 

 

 

A cewar Kwamared Suleiman kudirin ya kara bude wasu hanyoyi ga nakasassu wajen shiga harkokin Jama’a, Kula da lafiya, Ilimi, Aiki da Sufuri, yayin ƙirƙirar yanayi mai ba da dama ga Ƙungiyar tawaya jin daɗi don jin daɗin rayuwa mai kyau.

 

 

JONAPWD, ta yaba wa ƙoƙarin Gwamnatin Jiha don haɓaka haƙƙin Naƙasassu, kuma ta yi imanin cewa Dokar za ta tabbatar da haƙƙoƙi da gyaran al’amuran Nakasassu don cimma daidaiton damar da za a bai wa duk Al’ummar naƙasassu cikakkiyar damar shiga cikin harkokin al’umma baki daya.

 

 

Kwamared Suleiman, ya yi godiya ta musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufai, Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Rt Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani da Hon. Kwamishinan Ma’aikata da Ci gaban Al’umma.

 

 

Bugu da ƙari, JONAPWD sun yi godiya ga ƙoƙarin Tallafin Kwamitin Gyaran Jihar, Gamayyar Kungiyoyin (CALPED), Abokin Haɗin Gwiwar (PERL), Accountability Lab, Gidan Rediyon Kaduna da sauran ƙungiyoyi da Kafafen yada labarai da daidaikun mutane don gagarumar gudunmawar su ga aiwatar da dokar nakasassu ta jihar Kaduna.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.