Home / Garkuwa / Najeriya Na Bukatar Kowa Ya Bada Gudunmawarsa – Bafarawa

Najeriya Na Bukatar Kowa Ya Bada Gudunmawarsa – Bafarawa

 Imrana Abdullahi
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Dokta Attahiru Dalhatu Bafarwa, ya bayyana Najeriya a matsayin kasar da ke bukatar kowa ya bayar da gudunmawarsa da nufin dai- daita al’amura baki daya.
Alhaji Dokta Attahiru Dalhatu Bafarwa ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai
Bafarwa ya ce hakika Najeriya na matukar bukatar samun gudunmawar kowa domin da haka ne za a samu ciyar da kasar gaba, saboda a halin da ake ciki a yanzu korafe korafe sun yi yawa don haka yan siyasa su bari kowa ya kama kishin kasa kawai shi ne mafita.
A cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Alhaji Dokta Attahiru Dalhatu Bafarawa ( Garkuwan Sakkwato) da aka rabawa manema labarai ya ci gaba da bayanin cewa sakamakon irin cece- ku cen da ake yi game da batun kujerar shugaban kasa ya sa yan siyasa da masu bayanai a kan batutuwan al’amuran yau da kullum na fadin albarkacin bakinsu kan lamarin ina shugaban kasar Najeriya zai kasance.
Ya ce kuma hakan ya Sanya mutane da dama su na barin abin da ya dace kawai ana ta wadansu maganganun da ba ci gaba balantana kishin ciyar da kasa gaba.
Ya kara da cewa ya dace mutane musamman yan siyasa da masu fashin baki a kan al’amuran yau da kullum su Sani cewa magana a kan abin da ya shafi kasa ta yadda za a lalubo hanyoyin ci gaba su ne abin da ya dace ayi.
Ya ce lokaci fa ya yi da yan siyasa za su tabbatarwa da kawunansu cewa maganganu a kan batutuwan da suka shafi kasa ne abin yi don haka su rika magana a kan batun samun kyakkyawan shugabanci domin kasar Nijeriya ta zauna lafiya.
Ya dace dukkan yan siyasa da ke kowane bangare na kasar nan da su hada kansu wuri daya domin ciyar da kansu da kasa gaba. Ya zama wajibi kowa ya yi dukkan abin da zai yuwu ya bayar da gudunmawarsa ta fuskar samar da zaman lafiya da tsaro a kasa.
Hakika Najeriya na fama da matsalolin da suke zaman mata kalubale kamar irin matsalar Boko haram, fashi da makami,satar mutane,barazanar shiyya shiyya,rashin tafiyar da tattalin arzikin kasa kamar yadda ya dace lamarin da ya haifar da samun talauci,masu maganganun sake Fasalin kasa,kiraye Kirsten rarrabe kaza da kaza ko daga bangare kaza da kaza da dai sauransu.
Bafarwa ya ce a matsayinsa na dan siyasa a Nijeriya da za a iya ganinsu da kwarewar aiki a fannin siyasa da aikin Gwamnati ,ban san lokacin da aka kirkiro da batun tsayar da dan takarar shugaban kasa ta fuskar yin amfani da shiyya shiyya ba balantana wani ko wasu su rika yin wannan batu a hakan ko a Kudu ko Arewa ba don haka ba ni da wata masaniyar cewa jam’iyyun kasa na PDP ko APC sun furta cewa matsayin shugaban kasa an mayar da shi zuwa wata shiyya a cikin Najeriya.
Ya kamata yan siyasa su rungumi Akidar zama masu samar da dinke baraka a ko ina ake tsammaninta a fadin kasa ta yadda za a ci gaba da zama kasa daya al’umma daya.
Idan dai yan siyasa da masu fashin baki a harkokin siyasa za su ci gaba da yin kalamai a game da wane bangare ko shiyya ce za ta samar da shugaban kasa irin wadannan kalamai ka iya haifar da dumamar yanayi da kasa ke ciki.
Ya dace kowa ya rika Sanya kansa a kan ma’auni ya duba wace irin gidunmawa ce ya bayar domin ciyar da kasa gaba kuma me yakamata ya aiwatar a samu fita daga cikin halin da ake ciki mara dadi da ya dade ya na cewa kasar tuwo a kwarya.
Ya ce ba dai- dai ba ne wasu ko wani ya rika kokarin yin amfani da halin da ake ciki a rika yin siyasa da shi ko ganin wani tsari ko wani mulki ya kasa yin maganin yanayin da ake ciki ba.
 Halin tausayawa game da yanayin da ake ciki ne abin da ya dace kowa ya yi don haka ya dace a daina siyasantar da lamarin, yan Najeriya su zama masu Kaunar juna, masu son ayi zaman lafiya domin kare mutuncin kasar .
Ina ganin kokarin da muke yi na samar da zaman lafiya da Kaunar Juna zai samu nasarar da ake bukata a kasa , samun amintacciyar kasa mai zaman lafiya abin jin dadi ne kan batun dunkulewa wake daya.

About andiya

Check Also

Samar Da Tsaro Sai Kowa Ya Bayar Da Gudunmawarsa – Kaftin Joji

….A koma ga masu unguwanni, dagatai da hakimai Kaftin Muhammad Joji ya bayyana cewa lallai …

Leave a Reply

Your email address will not be published.