Home / Labarai / Rundunar Yan Sanda Sun Kama Matasa Takwas A Kano Dauke Da Wukake

Rundunar Yan Sanda Sun Kama Matasa Takwas A Kano Dauke Da Wukake

Yan Sanda Sun Kama Matasa Takwas A Kano Dauke Da Wukake

Imrana Abdullahi

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa mai magana da yawun rundunar yan Sandan ta kasa reshen Jihar Kano ya bayyana cewa rundunar ta samu nasarar kama wadansu matasa da ke amfani da wukake suna kokarin yi wa jama’a kwacen wayoyi a ranar Takutaha wato bikin Maulidin murnar haihuwar Annabi Muhammadu ( SAW).
Abdullahi Kiyawa ya dai bayyana ne a cikin wani faifan bidiyo inda ya tambayi matasan daya bayan daya yan tambayarsa sunansa da unguwar da yake da kuma wukar da yake dauke da ita, inda dukkansu suka tabbatar da cewa Wukar tasu ce baki daya.

Mai magana da yawun rundunar ya tabbatar da kama matasan guda Takwas (8) kuma a nan bada jimawa ba idan an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kuliya domin yi masu shari’a bisa laifin da suka aikata.
Ya ce tuni kwamishinan yan sandan Jihar Kano ya bayar da umarnin a kaiatasan sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike kuma a kamo sauran abokan aikata laifinsu a hada su baki daya domin fuskantar kuliya.

About andiya

Check Also

Trafficking: NAPTIP seeks more collaboration, advise potential victims

  By Suleiman Adamu, Sokoto The National Agency for the Prohibition of Trafficking in Person(NAPTIP) …

Leave a Reply

Your email address will not be published.