Daga Imrana Abdullahi
A kokarinsa na ci gaba da taimakawa rayuwar bil’adama ta inganta ya sa fitaccen Jagoran siyasa kuma fitaccen mai rajin taimakon al’umma, Yerima Shettima, ya halarci taron bada magunguna kyauta wanda kungiyar Yerima Shettima Support Initiative ta shirya a Asibitin Unguwan Rimi da ke jihar Kaduna.
Faruwar wannan lamari na aikin duba lafiyar jama’a da kuma ba su magunguna kyauta ya kara bayyana ƙarara a fili cewa wannan bawan Allah Shettima Usman Yerima, mutum ne mai kokarin ganin an inganta tare da bunkasa Rayuwar jama’a ta kowa ne fanni kamar yadda aka sani shi na rashin kare hakkin bil’ada da ya yi fice a wannan fanni da ya dauka tun ya na saurayi matashi har zuwa yanzu.
An dai yi wannan gagarumin taron duba lafiyar jama’a ne a karkashin gidauniyar sa ta Shettima Yerima wato, ( Shettima Yerima Foundation).
Tun lokacin da Shettima Yerima ke yin takarar Sanata Kaduna ta tsakiya yake yin irin wannan kokarin duba lafiya da kuma taimakawa jama’a ta fannin lafiya da sauran fannonin rayuwa.
A yayin taron, Yerima Shettima ya yabawa shugaban kungiyar Hussaini Usman tare da daukacin jagororinta bisa wannan gagarumin kokari na taimakawa marasa lafiya da marasa karfi a cikin al’umma. Ya bayyana cewa irin wadannan ayyuka na jin kai suna kara tabbatar da kaunar jama’a da kishin taimakon mabukata.
Ya kuma jaddada muhimmancin hada kai wajen tallafawa harkar lafiya musamman ga marasa galihu, yana mai cewa taimakon lafiya na daga cikin ginshikan inganta rayuwar al’umma.

Bayan kammala rabon magungunan, Yerima Shettima tare da tawagarsa sun zagaya sassa daban-daban na asibitin domin duba wadanda aka rabawa magunguna tare da jajanta musu da yi musu fatan samun sauki cikin gaggawa.
Al’ummar da suka halarci taron sun nuna farin ciki da godiya bisa wannan tallafi da aka kawo musu, tare da addu’ar Allah ya saka da alheri ga wadanda suka shirya wannan aiki na alkhairi.
An fitar da wannan sanarwa ne domin sanar da jama’a game da taron da kuma kokarin da ake yi na tallafawa marasa lafiya da mabukata a cikin al’umma.

Faruwar hakan zai kara tabbatar da cewa Alhaji Shettima Usman Yerima mutum ne mai kokarin fadi da cikawa kuma kamar yadda yake fadi ya na yi ne domin taimakon al’umma.
THESHIELD Garkuwa