Home / News / Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Muktar Ramalan Yero Ya Koma APC

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Muktar Ramalan Yero Ya Koma APC

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Muktar Ramalan Yero, ya tabbatar da komawarsa cikin jam’iyyar APC domin taimakawa Gwamnati ta cimma Burin kawo ci gaban al’umma baki daya.

 

 

Tsohon Gwamna Ramalan Yero ya bayyana hakan ne a wajen wani gagarumin taron manema labarai da ya kira a dakin ganawa da jama’a da ke cikin gidansa a Kaduna.

Tawagar jama’ar Muktar Ramalan Yero kenan

 

Ramalan Yero bayan ya yi wa Allah godiya ya ce hakika tsawon watanni biyar kenan da yake ta shawara tare da ganawa da jama’a da kuma jam’iyyu daban daban, amma dai a yau na yanke hukuncin komawa jam’iyyar APC tare da dimbin al’umma ta baki daya.

 

“Idan za a iya tunawa dai tun tsawon watanni biyar can baya na bayyana ficewa ta daga jam’iyyar PDP amma ban fadi inda zan nufa ba, ina ta tattaunawa da jam’iyyu daban daban da suka zo wuri na suna shawarci na,koda take jam’iyyar APC ce ta fara zuwa wuri na a ranar da na bayyana ficewa ta daga jam’iyyar PDP sai APC suka zo a ranar suna zawarcin in koma cikin jam’iyyar. To bayan a yau mun je gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, mun kuma yi magana da Gwamna Uba Sani da jama’arsa na kuma shaida masu cewa gani ni da jama’a ta bayan mun kammala tattaunawa da dukkan shawarar da za mu yi baki daya mun yanke shawarar komawa cikin jam’iyyar APC, don haka muka zo mu shaida maka hukuncin da muka yanke, Ramalan Yero ya kuma ce mun samu kyakkyawar tarba da karamci a lokacin da muka je gidan Gwamnati hakika an Karrama mu kwarai kuma muna godiya”.

Wasu daga cikin iyaye mata kenan da suka koma APC tare da tsohon Gwamna Muktar Ramalan Yero a Kaduna

 

“Sai dai ya shaidawa manema labarai cewa ba ya koma APC ba ne domin ya yi takara ba, mum koma ne domin taimakawa Gwamnati a samu ci gaban yi wa al’umma abin da ya kamata, wanda daman can shi ne Burin mu da na sauran jama’a”.

Tsohon Gwamna Ramalan Yero kenan a lokacin da suke tattaunawa tare da jama’ar da suka halarci taron tattaunawar kafin su yi taron manema labarai a gidansa

 

A cikin tawagar ta Ramalan Yero akwai wadansu yayan jam’iyyar Lebo da duka biyo tawagarsa suma sun koma APC tare da shi baki daya da suka hada da Maza da Mata.

 

Za dai mu ci gaba da kawo maku irin yadda tattaunawar ta kasance..

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.