Home / Labarai / GWAMNATIN BUHARI TA SAMAWA MATASA MILIYAN 4 AIKIN YI – NUHU FIKO

GWAMNATIN BUHARI TA SAMAWA MATASA MILIYAN 4 AIKIN YI – NUHU FIKO

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Abubakar Nuhu Fiko, shugaban hukumar samawa mutane aikin yi ta kasa ya bayyana Gwamnatin da Muhammadu Buhari ke yi wa jagoranci da cewa babu kamarta wajen samawa jama’a abin yi domin kowa ya Dogara da kansa.
Ya bayyana hakan ne a wajen bikin ranar hukumar da aka yi a kasuwar duniya ta Kaduna karo na 44 da aka yi a Kaduna.
Abubakar Nuhu Fiko wanda ya wakilci ministan kasa a ma’aikatar kwadago ta tarayyar Najeriya  Mista Festus Keyamo, ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari kwarai bisa kokarin da yake na ciyar da kasa gaba.
Abubakar Nuhu ya ci gaba da cewa Gwannatin Buhari ta taimakawa matasa miliyan hudu (4) sun samu abin yi, saboda haka ya cancanci jinjina kwarai.
 “Abin da Gwamnatin Buhari ta yi wajen samawa matasa aikin yi, babu Gwamnatin da ta yi shi”, inji Nuhu Fiko.
“Sakamakon Namijin kokatin da gwannatin Buhari ta yi ne yasa aka samu hukumar NDE ta taimakawa matasa miliyan 4 duk suka samu abin yi a karkashin mulkin Muhammadu Buhari”.
Abubakar Nuhu Fiko ya ci gaba da bayanin cewa “a can baya hukumar na a cikin wurin gidan haya da ake kashe miliyan 60 na kudin haya, amma a yanzu Gwamnati ta ba mu sama da biliyan biyu domin mu kammala aikin matsugunnin mu na dindin din”.
Muna da cibiyoyin Koyar da sana’o’i a ko’ina a Najeriya da ake bayar da shawarwari kafin a fara koyawa jama’ a aiki domin su dogara da kansu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.