Home / Big News / Kungiyar Matasan Kiristoci Kwararru Na Taya Zababben Shugaban Kasa Bola Ahmed Murnar Sallar Eid – el – Fitri

Kungiyar Matasan Kiristoci Kwararru Na Taya Zababben Shugaban Kasa Bola Ahmed Murnar Sallar Eid – el – Fitri

 

….A Tabbatar Da An Ba Kwararru Mukaman Da Za A Nada

 

Kungiyar Matasan Kiristoci Kwararru da ke arewacin Najeriya (NCYP) na mika sakon farin ciki tare da murna ga zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu game da zagayowar ranar Sallar Eid- El- fitar.

 

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Isaac Abrak Shugaban kungiyar matasan kwararrun kiristoci (NCYP).

Kungiyar ta ci gaba da bayanin cewa sun lura wannan bikin murnar karamar Sallar ya zo ne a lokacin wani tarihi a rayuwarsa da kuma tarihin Najeriya da zai kasance ya zamo shugaban kasa bayan kammala Azumin watan Ramadana, da musulmi suka yi Ibadar da ta fuskantar da su ga Allah madaukakin Sarki.

Don haka kamar yadda muke bikin taya Tinubu, murna, muna kuma yi masa tuni da cewa yan Najeriya ne fa suka zabe shi saboda irin tarihin nasarar ayyukan da ya samu a lokacin ya na Gwamnan Jihar Legas da ya samawa daukacin al’umma romon mulkin Dimokuradiyya.

Tinubu ya bunkasa Jihar Legas inda ta zamo daya daga cikin birane mafiya bunkasar tattalin arziki a nahiyar Afirka saboda ya samo mutane masu aiki tukuru da suka san abin da suke yi ta fuskar yin aiki tsakani da Allah da nufin ci gaban al’umma baki daya.

Saboda haka ne muke bayar da shawara cewa idan zai samo mutanen da zai yi aiki da su a matsayinsa na shugaban kasa da ya zabo su daga kowane bangaren al’umma ba tare da yin la’akari da kabila ko addinin da suka fito ba a dai tabbatar da zaben mutanen da suka cancanta kawai.

Hakan ne yasa muke yin tuni ga zababben shugaban kasa da kada ya yi sako – sako da zaben wadanda suka cancanta wajen zaben mutanen da za su yi aiki da shi da suka fi kusa da shi, masu bashi shawara da sauran manyan jami’an Gwamnati a matsayin shugaban kasa.

Hakika wannan samun kwararru masu aiki tukuru ne yasa yan Najeriya suka zabe shi, don haka ana saran samun kyakkyawan sakamako koma abin da ya fi wanda ake tsammani.

Kungiyar NCYP ta lura cewa samun shugabancin Tinubu ya zo ne a lokacin da yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki da matsalar tsaro mai tsananin gaske saboda haka ne ya dace a Sani cewa kasar ba za ta zauna a haka ba balantana yanayin da take ya wuce abin da take ciki .

Don haka, Muke kara fadakar da al’umma baki daya cewa dole sai an samu wadanda keda kokarin yin aikin sa kai domin kasa ta ci gaba kamar dai irin wadanda suka yi aiki da Tinubu lokacin da yake Gwannan Jihar Legas.

Idan an samu hakan lalle za a samu ci gaban da ake bukatar samu domin kasa da al’ummarta za su ci gaba har a fita daga cikin halin da ake ciki, kamar dai irin yadda shugaban farko suka yi mafarkin za a samu ci gaba a kasa.

Haka kuma kungiyar NCYP na taya dukkan daukacin musulmi murnar Eid- El- fitr, muna kuma yin kira ga daukacin yan Najeriya da su kara dukufa wajen yin addu’a ga sabon zababben shugaban kasa da kuma samun mika mulki cikin nasara a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.

 

 

 

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.