Home / Labarai / Zan Dukufa Wajen Bullo Da Sauye-Sauye A Bangaren Shari’a da Na Hukumomi Don Inganta Shugabanci Nagari –  Buni 

Zan Dukufa Wajen Bullo Da Sauye-Sauye A Bangaren Shari’a da Na Hukumomi Don Inganta Shugabanci Nagari –  Buni 

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe a bikin Rantsar da shi a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Yobe na tsawon shekaru hudu da babban alkalin jihar, Mai shari’a Gumna Kashim Kaigama ya yi ya tabbatar da cewar, a wannan lokaci zai daura damara tare da dukufa wajen bullo da sauye – sauye a bangaren shari’a da na sauran hukumomi da ke jihar don inganta shugabanci nagari tare da rikon amana.
A cikin  jawabinsa na bikin rantsar da shi da rantsar da shi, Gwamnan ya kara da cewar, haka nan sabuwar gwamnatinsa za kuma ta jawo hankalin masu zuba jari da kuma saukaka harkokin kasuwanci a Jihar tare kuma da sake  inganta tsarin SULHU a matsayin ginshikin tsarin warware duk wata takaddama da kan iya tasowa don samar da zaman lafiya mai daurewa, a Jihar.”
Ya yi amfani da dandalin wajen gode wa ‘yan kasa bisa wannan sabon wa’adin da aka yi mana “Ina godiya ga ’yan uwanmu, mutanen Jihar Yobe, da suka sake zabar mu don ganin cancantar mu a wani wa’adin mulki kuma suka ba mu wannan dama, Lallai mu masu godiya ne.”
“Don haka  Ina mika hannun zumunci ga kowa da kowa don mu hadu  a aikin gina Jihar ta mu ta Yobe.  Wajibi ne mu ma mu yi kokarin sauke Wannna nauyi tare da taimakon Allah SWT da kuma ku wadanda kuka sake zabo mu.”
“Gwamnan ya kuma mika godiyar sa ga dukannin  masu ruwa da tsaki dake Jihar dangane da yadda suka sadaukar da kai wajen ganin jihar Yobe ta samu zaman lafiya da ci gaba, ba tare da la’akari da wani bambanci ba”.
“Ina mika godiyata ga ’yan Majalisar Dokokin Jihar a daidaiku da kuma a baki daya saboda kyakkyawar alakar aiki da bangaren zartarwa da na shari’a na gwamnati wadda  duk irin nasarorin da muka samu sun kasance saboda goyon bayansu da hadin kai da muka samu ne daga gare su,  Ina taya su murna da nasarar zaben da aka yi a babban zaben da ya gabata,  Ina kuma neman da su ci gaba da ba mu goyon baya tare da hada kai domin ganin Yobe ta zama abin alfaharin yankin Sahel.”
Buni ya taya “Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR murnar zama shugaban tarayyar Najeriya na 16, da kuma dan uwana, Kashim Shettima, GCON, a matsayin mataimakin shugaban kasa.  Shugaba Tinubu ya cancanci a zabe shi, fiye da kowane dan takarar shugaban kasa, ganin cewa shi ne kan gaba wajen maido da dimokuradiyya a Najeriya.
Don haka a madadin daukakin mutanen jihar Yobe, ina tabbatar masa shi da mataimakin shugaban kasa kan cigaba da jajircewa don nuna goyon bayanmu kan manyan ayyuka da ke gabanmu”.
Gwamna Mai Mala Buni ya lissafo wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannonin ilimi, samar da kiwon lafiya, noma, kasuwanci, samar da ababen more rayuwa, gidaje masu tarin yawa, albarkatun ruwa da muhalli, bunkasa albarkatun ma’adinai, gudanar da mulki da bin doka da oda da dai sauransu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.