Daga Imrana Abdullahi
A ci gaba da rangadin fahimtar juna ga kungiyoyin yada labarai a Kaduna, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kaduna, ya tabbatar wa ‘yan jihar kan kudirin Gwamna Uba Sani na cika alkawuran da ke kunshe a cikin littafinsa na “SUSTAIN manifesto”.
A cikin wata sanarwar da ke dauke da Sa hannu Mock Samuel Kure
Babban mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin jama’a da aka rabawa manema labarai ta ce
Babban jami’in yada labaran Gwamnan Jihar Kaduna ya jaddada mahimmancin kafofin yada labarai a matsayin muhimmin bangare na al’umma da kuma muhimmin bangare na dimokuradiyya.
Sai ya kuma Ya bayyana muradin gwamnati na kulla alakar hadin gwiwa da kafafen yada labarai don inganta kyawawan manufofin gwamnati da take aiwatarwa domin jama’a.
Ya ce Gwamna Sani ya san yana da tsarin da zai dace da kafafen yada labarai, da manufofin bude kofa, da gudanar da harkokin mulki na bai-daya. Bayanin da ke kunshe a cikin kundin da zamu yi aiki da shi da ya bayyana cikakken shiri ne da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar Kaduna.
Malam Shehu wanda shi ne babban jami’in yada labarai ma Gwamnan Jihar Kaduna ya bukaci kafafen yada labarai da su ci gaba da taka rawar masu sa ido kan al’umma tare da dorawa gwamnati alhakin.
Ya kuma yi kira da a hada kai wajen inganta shugabanci nagari da ci gaban jihar Kaduna.
Gidajen yada labaran da aka ziyarta sun hada da Nagarta Radio, Vision FM, AIT/Raypower, DITV/Alheri Radio, Correct FM da Invicta FM duk da suke a cikin garin Kaduna.
Shuwagabannin kungiyoyin yada labarai a nasu jawabin sun yi alkawarin tabbatar da mafi girman yada manufofi da shirye-shiryen gwamna Uba Sani, domin fadakarwa da wayar da kan al’umma kan tasirin da manufofin ke da shi ga jihar. Sun kuma yi alkawarin samar da sahihin rahotanni na ayyukan gwamnati ba tare da son zuciya ba.