Daga IMRANA ABDULLAHI
Kamar dai yadda jaridar theshieldg.com da ke a yanar Gizo ta wallafa cewa dan majalisar da ke wakiltar karamar hukumar Chikun a majalisar dokokin Jihar Kaduna Madami Garba Madami ya rasu kwanaki uku kacal da Rantsar da su a matsayin zababbun yan majalisar da suka lashe zabe a shekarar 2023.
An tattaro cewa Madami ta rasu ne a safiyar ranar Asabar yayin da yake jinyar rashin lafiya da ba a bayyana sunanta ba.
Shi dai marigayi zababben dan majalisa Madami Garba Madami, kafin rasuwarsa ya kasance zababben dan majalisar jiha, Madami ya kasance tsohon shugaban karamar hukumar Chikun a karkashin jam’iyyar PDP, kuma tsohon kwamishinan tsare tsare da tattalin arziki na Jihar Kaduna kuma mai bayar da shawara ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna marigayi Patrick Ibrahim Yakowa.
Ya kuma taba zama tsohon kwamishinan tsare-tsare na tattalin arziki a jihar.
Wannan al’amari na rasuwar zababben dan majalisa kwanaki uku bayan an Rantsar da su a matsayin zababbun yan majalisar Jihar Kaduna ya kasance wani wa’azi ne mai cike da fadakarwa da kowa zai yi zurfin tunani a kansa musamman irin dimbin darasin da ke tattare da lamarin.